21
Dec
Daga DAKTA ALIYU U. TILDE Shawarar da Ɗan Majalisar Tarayya, Alhaji Gudaji Kazaure, ya bayar na dakatar da gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, tana da kyau sosai kuma tana bisa ƙa’ida. Kai, ma iya cewa ma ta zama babbar buƙatar ƙasa a yanzu. Idan ba a ɗaga kaza daga makwancinta ba, ba za a san me fukafukanta suka boye ba. Don haka, ƙa’ida ce mai kyau idan za a yi bincike mai zurfi musamman idan wanda yake shugabantar wurin yana nuna tirjiya da ƙoƙarin danne gaskiya, to a dakatar da shi. Shugaba Buhari ya sa Honarabul Kazaure aikin bincike a…