17
Dec
Ƙuri’ar ’yan ƙasa da shekaru 18 wata ɓarna ce a tsarin zaɓen Nijeriya. Shekarun da suka cancanci shiga zaɓe a ƙasar sune ’yan shekaru 18 zuwa sama. Sai dai a lokacin zaɓe, ana barin yara su kaɗa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar. Wani lokaci ma matattu ma suna yin zaɓe. Kuma wannan shine tushen fara rigingimu. Lokacin da aka ba wa yaran da ba su kai shekarun jefa quri'a damar jefa ƙuri'a ba, hakan yana kawo cikas ga sahihancin tsarin zaɓe kuma yana sanya alamar tambaya kan sakamakon aikin. A kwanakin baya, gamayyar ƙungiyoyin farar hula 10 (CSO) sun koka…