Da Ɗumi-Ɗumi: Gobe take Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da cewa ya samu sahihan rahotanni daga sassan ƙasa dangane da ganin watan Ƙaramar Sallah.

Don haka idan Allah Ya kai mu gobe Juma’a, take 1 ga watan Shawwal, 1444 AH wanda ya zo daidai da 20 ga Afrilu, 2023.

Kwamitin tantance ganin wata ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan.