FOMWAN ta buƙaci reshenta na Bauchi ya kafa manyan makarantu

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Ƙungiyar Mata Musulmi Ta Nijeriya (FOMWAN) ta buƙaci reshen ta na jihar Bauchi ya kakkafa manyan makarantun koyar da ilimi a cikin jiha domin bunƙasa cigaban ilimin mata da matasa.

Kamar yadda Amirar ƙungiyar ta ƙasa, Rafi’at Idowu Sanni ta ce, ire-iren waɗannan manyan makarantu kamar Jami’ar Koyon Haɗa Magunguna ko Kwalejin FOMWAN kan likitancin ungozomanci (HealthTechnology) da Cibiyar fasahar Sadarwa (ICT), da makamantansu.

Amira ta qasa ta ƙungiyar FOMWAN tana jawabi ne a yayin buɗe gangami akan ilimi na kwanaki biyu da reshen qungiyar na jihar Bauchi ta shirya mai taken “Cimma Muradun Cigaba Ta Hanyar Ingantaccen Ilimi A Cikin Ƙalubalolin Rashin Tsaro” wanda aka gudanar a ɗakin taro na babban masallacin Bauchi a makon da ya gabata.

Amira Rafi’at Sanni ta bayyana cewar, FOMWAN tana da ginshiƙan manufofi guda biyar waɗanda suka haɗa da bayar wa mata ilimi, bayarnwa ‘yan mata ilimi da sadaukar da kai wa ayyukan al’umma, da sauran su.

Amirar ƙungiyar ta ƙasa tanyi la’akari da cewar, gangami kan ilimi yana ɗaya daga cikin hanyoyi da ƙungiyar ta zayyana domin faɗakarwa da nusar da al’umma, musammman masu ruwa da tsaki a fannin ilimi ta yadda za su bayar da muhimmanci ga lamuran neman ilimi.

Ta jinjina wa mambobin kwamitin ilimi na reshen ƙungiyar da ke Bauchi bisa ƙoƙarin su na kakkafa makarantun nazare, firamare da sakandare a sassan jiha, tana mai jaddada buqatar a bai wa yara maza da mata damar bai ɗaya ta neman ilimi.

Rafi’at ta nuna farin cikin ta na cewar, lokaci tuni ya shuɗe na kallon ƙungiyar da ƙasƙancin rashin ilimin mambobin ta, domin a yanzu FOMWAN tana da mambobi masu digiri har ma da masu digirgir masu ɗimbin yawa.

Ta kuma bayyana FOMWAN a matsayin qungiya mai fafutiukar bunƙasa ilimin mata, matasa da kuma yara ta hanyar kakkafa makarantu daban-daban, har ma dana koyon sana’o’i a dukkan sassan ƙasar nan.

Da take buɗe gangamin akan ilimi, uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya A’isha Bala Mohammed ta bayyana cewar, gwamnatin Ƙauran Bauchi tun lokacin da ta hau kan karagar mulki tana bai wa fannin ilimin mata da matasa muhimmanci da ya kamata.

Uwargidan gwamnan wacce ta samu wakilcin kwamishina mai lura da lamuran mata da ci gaban yara Hajara Jibrin Giɗaɗo, ta bayyana cewa gwamnatin jiha a koyaushe tana ƙwamutsar ƙungiyoyi masu zaman kan su kamar FOMWAN wajen assasa cigaban ilimi a jihar ta Bauchi.

Tunda farko a jawabin ta na marhabun, Amirar ƙungiyar ta jiha, A’ishatu Ibrahim Kilishi ta lura da cewar, neman ilimi ya zarta koyar da matasa karatu da rubutu kaɗai, domin ilimi wani ginshiƙi ne na shimfiɗa zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Hajiya A’ishatu Kilishi da take bayar da tabbacin FOMWAN za ta cigaba da yaɗa ilimi a cikin al’umma, ta bayyana cewar, ilimi yana da matuƙar muhimmanci a walwala da tattalin arziki, siyasa, kimiyya da fasahar kowace al’umma a nan doron ƙasa.

Kilishi, ta kuma bayyana cewar, ilimi shine jigo na kore talauci da kuma bunƙasa cigaban al’umma, tana mai cewa FOMWAN a jajirce take wajen samar da damammakin neman ilimi, la’akari da cewar, ta kakkafa makarantun nasare, firamare da sakandare guda 14 a sassan jiha, cibiyoyin Islamiyya da koyon Al’ƙur’ani fiye da guda 100, ajujuwan neman ilimi na manyan mutane guda 15, haɗi da cibiyoyin koyan sana’o’i daban-daban.

Hajiya Kilishi ta ce ƙungiyar FOMWAN ta hankaltu matuƙa gaya da samar da ilimin ‘ya’ya mata, da malaman da ke karantar da yara waɗanda sune babban jari na kawar da talauci, jahilci da cutattaki.

Ta yi la’akari da cewar, fannin ilimi a jihar Bauchi yana fuskantar ƙalubaloli daya kamata a daƙile su, tana mai faɗin “Mun fahimci ƙarancin kuɗi, nakasun aiwatar da manufofin ilimi, siyasantar sa fannin ilimi, rashin alkintawa, banzatarwa, ƙarancin bayanai sunadaga cikin matsaloli dake jawo wa neman ilimi koma-baya.

Kilishi ta ƙara da cewar, “Ilimi wani jigo ne na inganta tsaro a ƙasa. Yana taka matuƙar rawa wajen wanzar da kyakkyawan tsaro da zama lafiya. ilimi daya gwamatsi lamuran tsaro ya zarce batun koyar da karatu da rubutu kaɗai, lamari ne gama-gari.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *