Giɓin zaɓe: Sufeto Janar ya bayar da tabbacin tsaro ga masu zaɓe

Usman Baba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin sake zaɓen da za a yi ranar Asabar a runfunan zaɓe 2,660 a faɗin ƙasar nan, Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Usman Baba ya ba wa masu kaɗa ƙuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zaɓe.

Ya kuma ba da umarnin tura ’yan sanda zuwa ƙananan hukumomi 185 a faɗin jihohi 24 na tarayya inda za a sake gudanar da zaɓen ranar Asabar.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a lokacin zaɓukan 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris ta bayyana wasu zavukan gwamnoni da na majalisun tarayya da na majalisun jihohi da ba su kammalu ba, tare da ba da umarnin sake zaɓen.

Rikicin da ya carke da murƙushe masu kaɗa ƙuri’a ya haifar da cikas a zaɓukan 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, musamman a jihohi kamar Legas, Ribas, da dai sauransu yayin da ’yan baranda suka yi ta’addanci kan masu kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe, lamarin da ya ƙara rura wutar rashin jin daɗin masu zaɓe.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Muyiwa Adejobi, ya ce shugaban ’yan sandan ya ba da umarnin aikewa da isassun jami’an da ke tallafawa da kuma ƙarin kayan aiki don gudanar da ingantaccen tsaro a zaɓen da za a gudanar a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.

A wani ɓangare sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙarin tallafin ya haɗa da tura ma’aikata, motocin aiki, muggan makamai, kayan kariya na sirr, kayan yaƙi da tarzoma da dai sauransu.

“Haka zalika, IGP ya umurci dukkanin manyan jami’an ’yan sanda da ke kula da hukunce-hukuncen da za a gudanar da zaɓuɓɓukan ƙarin zaɓe, musamman zaɓen gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi, da su tabbatar da samar da isassun ma’aikata da sauran kayan aiki don yin tasirin aikin ’yan sandan tsarin zaɓe.”

IGP ɗin ya buƙaci masu zaɓe a jihohin da abin ya shafa da su fito gaba ɗaya domin yin amfani da ikonsu da kuma bin doka da oda tare da wanzar da zaman lafiya.