Gobara ta kashe ɗalibai 20 a Guyana

Rahotanni daga yankin Guyana a Amurka ta Kudu sun ce, aƙalla ‘yan mata 20 sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wata makarantar mata da ke yankin.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani cikakken bayani kan abin da ya haifar da gobarar.

Bayanai sun nuna ɗaliban da lamarin ya shafa ‘yan mata ne ‘yan shekara tsakanin 11-12 da kuma 16-17.

Iftila’in ya auku ne a ƙarshen makon da ya gabata.

A cewar jami’an yankin, “Mutum 14 ne suka mutu nan take, yayin da shida suka cika a asibiti.”

An ce ɗalibai 63 ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, sannan waɗanda suka jikkata na ci gaba da karɓar magani.

Guyana, ƙasa ce mai yawan al’umma kimanin 800,000. Kuma ita ce ƙasa ɗaya tilo da ake amfani da harshen Ingilishi a yankin Amurka ta Kudu.