Matsayar ƙasar Sin dangane da batun Ukraine, ta jaddada matsayinta na babbar ƙasar da ta san ya kamata

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Ƙasar Sin ta sake jadadda matsayarta game da batun Ukraine da Rasha. Inda ta nanata cewa, bata neman cimma wani muradi na son kai a siyasar duniya dangane da batun, haka kuma, bata nuna halin ko in kula, bare kuma ta nemi kara rura wutar rikicin. Haƙiƙa, wannan ya sake fito da matsayin ƙasar Sin na babbar ƙasa da a kullum take kira da hawa teburin sulhu don tattaunawa da zummar samun maslaha, maimakon haddasa fito na fito.

Ƙasar Sin ta bayyana haka ne ta bakin mamban majalisar gudanarwar ƙasar kuma ministan harkokin wajenta Wang Yi, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba.

Tattaunawar wadda irinta ce ta biyu tun bayan ɓarkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine, ya ƙara tabbatar da matsayin ƙasar Sin mai sanin abun da ya kamata, domin ta tsaya ne tsayin daka wajen tuntubar kowanne ɓangare da zummar lalubo bakin zaren rikicin maimakon nuna ɓangaranci ba tare da bada wata gudunmuwa na kawo ƙarshen fitinar ba.

Kamar yadda Wang Yi ya bayyana, ainihin abun da Sin take sa rai game da yanayin Ukraine shi ne zaman lafiya. Wato bata da wani buri da ya wuce zaman lafiya a duniya. Ingiza tattauanwar zaman lafiya da take yi tsakanin ɓangarorin biyu, manuniya ce cewa bata da wani abu da take burin samu daga rikicin.

Ƙasar Sin ta sha nanata cewa, bata da wata riba daga faduwar wata ƙasa a duniya. Wannan haka yake, domin shaidu sun nuna cewa, hanyar ta na neman ci gaba, ya bambanta da na sauran manyan ƙasashe, domin tana raya kanta ne bisa nata tsarin a cikin gida ba tare da takurawa ko mulkin mallaka ba. Lamarin da ba sai an fada ba, ya kai ta ga samun ci gaba cikin sauri har take da babban matsayin a idon duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *