Pantami ya buƙaci matasa su mayar da hankali kan fasahar ƙirƙira

Daga UMAR GARBA a Katsina

Pantami ya buƙaci matasa da su mayar da hankali akan sana’ar fasahar ƙirƙira a madadin dogaro da takardar shaidar kammala karatu. 

Ministan Sadarwa na Nijeya, Isah Aliyu Pantami ya buƙaci gwamnati, matasa da sauran al’ummar ƙasar nan akan su mayar da hankali  wajen koyon sana’ar ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar zamani a madadin mayar da hankali a kan takardar shaidar kammala karatu don samun ayyukan dogaro da kai.

Pantami ya bayyana haka ne a sakatariyar gwamnatin jihar Katsina a wajen wani taron bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara a gasar zaƙulo matasa masu baiwar ƙirƙirar fasahar zamani a ƙarƙashin shirin zaƙulo matasa masu baiwa da ƙirƙira ta musamman ta ƙasa a Jihar Katsina, wato “Katsina National Hunt Talent Challenge”, wadda  gwamnatin jihar Katsina ta shirya.

A cewar sa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta matsa ƙaimi wajen taimaka wa masu baiwar ƙirkireƙirƙire don fito da shirye-shirye daban-daban ga ‘yan ƙasar nan domin su zama masu dogaro da kai.

Ya kuma bayyana cewar mayar da hankali akan zaƙulo masu baiwar fasahar ƙirƙire-ƙirƙiren abubuwan zamani zai samar da ayyuka a tsakanin al’umma tare da shawo kan matsalar rashin ayyukan yi a ƙasar nan.

A jawabin Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar maƙasudin shirya gasar shine domin a zaƙulo matasa masu baiwar ƙirƙira a jihar Katsina da ma ƙasar nan baki ɗaya domin a ƙarfafa masu gwiwa gami da tallafa wa baiwar da Allah ya yi masu.

Gwamnan ya kuma bayyana nasororin da gwamnatinsa ta samu a ɓangaren samar da ayyukan yi ga matasa, ta hanyar koyar da su sana’o’i da bada jari, a ɓangarori daban-daban a faɗin Jihar Katsina. 

A nashi jawabin Shugaban Hukumar Bunƙasa Fasahar Taswirar Ƙera Motoci ta Ƙasa, Malam Jelani Aliyu ya bayyana cewar babu shakka shirya gasar wata muhimmiyar dama ce ga matasan jihar Katsina don bayyana baiwa da fasahar da Allah ya ba su.

A cewar sa wannan zamani da ake ciki ya zama wajibi ga kowace jiha a arewacin Nijeriya ta yi koyi da gwamnatin Jihar Katsina don zaƙulo matasa masu baiwa da fasaha a fannoni daban-daban, don a tallafa masu, su ƙirƙiri wata sana’a da za ta zama abin dogaro a gare su.

Shirin ya kasu kashi huɗu, wanda su ka haɗa da, masu baiwar zane-zane, da masu baiwar kiɗa da waƙa, masu sanin fasahar zamani, masu baiwar ƙirƙirar mota, babur da sauran ƙere-ƙeren zamani makamancin haka.

Kowane ɓangare  ya samu kyautar kuɗi inda na ɗaya ya samu kyautar Naira miliyan 5 na biyu ya samu kyautar Naira miliyan 3, sai wanda ya zo na uku ya samu kyautar Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar.

Sai wanda ya zama zakaran gasar ɓangaren sanin fasahar zamani wato  (ICT) Abdulhakim Bishir daga ƙaramar hukumar Katsina ya samu kyautar mota ƙirar Toyota Highlander Jeep da kuɗi Naira miliyan 2.

Haka zalika mutane ɗari da su ka shiga gasar, waɗanda ba su samu nasarar shiga cikin kashi huɗu na manyan kyaututtuka sun samu kyautar Naira dubu ɗari, kowannensu.

Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina wanda ya samu wakilcin ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, Arc.

Ahmed Musa Ɗangiwa, Gwamnan Jihar Kano wanda Kwamishinan Ilmi na Jihar ya wakilta gwamnan Jihar Neja wanda ya samu wakilcin kwamishinan Ilmi na jihar da dai sauran manyan baƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *