PDP ta lashe kujerar Majalisar Wakilai a mazaɓar Fune/Fika a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

Ɗan takarar Majalisar Wakilai a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Engr. Mohammed Buba Jajere, ya lashe zaɓen Majalisar Wakilai a mazaɓar Fune/Fika da ke jihar Yobe.

Da yake sanar da sakamakon zaɓen a garin Damagum, shalkwatar ƙaramar hukumar Fune, Baturen zaɓen, Farfesa Johnson Sunday Alao, ya ayyana jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta samu ƙuri’u 32,464.

Ya ce APC ta samu ƙuri’u 31,969, NNPP 1011, ADC 400, YPP 125, SDP 108 da jam’iyyar AA mai ƙuri’u 78.