Rashin tallafi kan iya durƙusar da harkar noman albasa – Aliyu Mai-ta-samu

Daga AMINU AMANAWA a Sokoto

Albasa ɗaya ce daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa abinci ko kuma sarrafa magunguna da sauran kayan maƙulashe. Nijeriya ƙasa ce da ke kan gaba a nahiyar Afirka wajen noma da ma sarrafa albasar. Da alama a Najeriya, Jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma, ce ke jagorantar jihohin ƙasar wajen noman albasar, abinda ma ya sa dubban matasa da dattawa samun hanyar dogara da kai kama daga masu noma, kasuwanci, dako, sufuri, dillanci da makamantansu. Sai dai kash! duk da muhimmanci da rawar da noma da kasuwancin albasar ke takawa, manoma albasa a Najeriya na nuna damuwarsu matuƙa kan yanda gwamnatoci na dukkanin matakai suka maida su saniyar ware wajen tallafa wa manoman albasar domin bunƙasar da harkar tasu, duk kuwa da cewa wasu lokuta suna gamuwa da jarabawar rayuwa ta yin asara. Wakilin Blueprint Manhaja a Sakkwato, Aminu Amanawa, ya zanta da Shugaban Ƙungiyar Masu Noma da Kasuwancin Albasa na Ƙasa, Alhaji Aliyu Mai-ta-samu Isa, wanda ya nuna damuwarsa sosai kan rashin tallafa masu, duk da cewa sun sha tafka asara inda ko a shekarar 2019 manoman albasar na jihohin Sokoto da Kebbi kaɗai sun yi asarar fiye da Naira biliyan biyu. Ga yanda zantawar su takasance.

MANHAJA: Da farko ka gabatar da kanka
MAI-TA-SAMU: Sunana Alhaj Aliyu Mai-ta-samu Isa Shugaban ƙungiyar masu noma da kasuwancin albasa na Nijeriya

Daminar bana na ƙara kankama, bayan da wasu jihohin ma ta daɗe da kankama ya shirye-shiryen noman albasa na wannan shekarar?
Alhamdulillah ita Albasa da ma muna noman ta sau 3 a shekara, watau noman rani, damina da kuma kaka sai dai noman rani ne babban noman da muka fi noma albasa, shi ya sa ma kake ganin ba a cika samun yankewar albasa ba a kowane lokaci a kasuwanni, duk da cewa muna noman daminar amma gaskiya ba mu cika yinsa sosai ba tamkar na rani da kaka. Amma duk da haka, akwai wuraren da suke noman albasa ta damina musamman ƙananan hukumomin kudancin Sokoto irin su Dange-shuni, Bodinga, Tambuwal, Yabo, Shagari da sauransu, su ne suke noman albasa sosai . Shi ya sa suke da babbar kasuwar da ake hada-hadar albasar ta Bodinga. Nan kuma gabascin Sokoto akwai irin su Gada, Giyawa, Lugu, shi ya sa ma dai Sakkwato ta zama uwa wajen albasa a duk faɗin Nijeriya ba jihar da ta kai Sokoto wajen noman albasar.

Shin a Sokoto ne kawai ake noman damina na albasar?
A’a, da akwai jihohi irin su Kaduna, Kano, sun ma fi noman albasar damina sai dai albasar damina ba ta kai ta rani inganci ba. Amma idan ka duba idan ba noma ake irin haka ba yanda ake amfani da albasa ba a iya cimma buƙatu na mutane kan albasar, domin ita ba abu ba ce da idan ka yi amfani da ita, za ka ce ba za ka sake amfani da ita ba sai wani sati, a’a abu ce da koyaushe ana da buƙatar ta sosai kuma kusan koyaushe. Ta vaingaren shiri kuwa, da akwai haɗaka da muka soma da babban bankin Nijeriya (CBN) na za su bamu rance mu bawa manomanmu kusan dubu 20,000, duk da har yanzu dai shiru ba a cimma matsaya ba.

Kuma kasan dama manoma yanzu na cikin wani hali musamman ma ƙananan manoma. Tattalin arzikinsu na cikin wani hali, idan ba taimako aka samu ba. Sai ka ga ana fuskantar matsala da kuma kasawa to irin wannan lokaci ne da muke son gwamnati ta riƙa tallafawa, saboda kauce wa shafuwar shi tattalin arziki kansa.

Inda aka fito na san manoman albasa sun fuskanci ƙalubalai irin na gobara da sauransu, wannan ba zai shafi noman albasar ba?
Idan ka duba irin haka ai ta faru a shekarar 2019 da aka fuskanci sauyin yanayi kan daminar wannan shekarar ya sa cutar da muke kira “Dan Zazzalau” ta kama albasar manomanmu a Sokoto da Kebbi da muka yi asarar sama da naira biliyan biyu, mukayi ta korafi kan a tallafa mana amma akaki tallafawa duk da irin muhimmanci noma da kasuwancin albasa ga tattalin arzikin kasa, amma aka yi ko oho. Manoman sun shiga wani mawuyacin hali fiye da yanda kake zato amma ba a tallafa mana ba. Kai lokacin kan tsananin buƙatar albasa, har ƙasar Indiya ta rubuto mana buƙatar albasa. kaga da an tallafa mana da manomanmu za su amfana da ma ƙasa ita kanta, amma idan aka ce ga wata matsala gwamnati ta kasa tallafawa, sai ka ga ‘yan kasuwa sun shiga cikin wani hali, kasuwancin ma haka da sauransu.

Kamar irin haka na shafar manoma kenan?
A yadda noman albasa ke tafiya kamar ace ne na sama ne ke taimaka wa na ƙasa, misali ka ga Sarkin noman albasar sarkin musulmi yana da sama da mutum 50 da yake bawa bashin kaya irin su iruruwa, taki, magani suyi noma, to idan aka samu wata jarabawa ta faɗar wa wannan babban dake taimaka wa ƙananan manoma, to idan ba a taimaka masa ba, ba’a kuma taimaka wa na ƙasa ba, sai ayi haihuwar guzuma: Ɗa kwance, uwa kwance, to haka yanayin noman albasar yake. Sai ka ga abinda y akamata a samu na noman a wannan shekarar, ba a samu ba. Shi ya sa ko a wannan shekarar mun faɗa wa Duniya cewa, za a iya shiga cikin wannan matsalolin. Kuma idan ka duba tuni aka kama hanyar shiga waɗannan matsalolin.

Shugaba wani zai yi mamaki ganin duk da muhimmancin noma da kasuwancin nan naku, kuna ƙorafin rashin samun tallafi. Shin ba kwa bin matakan da suka dace ne wajen neman tallafin, ko kuwa dai tallafa maku ne ba a yi?
Ai ku ‘yan jarida ku za ku zama shaida a kan hakan na duk abinda yakamata a ce a yi, muna yi. Sai dai mun tsinci kanmu ne cikin yanayin da gwamnatocin ba sa tallafa mana. Mun sha kawo misalai idan kace kana son saka hannun jari a harkar Shinkafa, duk yadda ka yi, ba za ka wuce Kebbi ba. Haka in ka dauko gero ba ka wuce Yobe, citta: Kaduna, dankalin Turawa, Jos. Amma idan ka ɗauko albasa, ba yadda za ka wuce Sokoto. To sai masana ɓangaren tattalin arziki suka ce, idan ka gano haka sai ka mai da hankali a gurin da kake ganin idan ka saka jari zai yi ƙarfi har ma a ci riba, ta hanyar noma da ma sarrafa albasar. To sai ya zamana ita albasar muna nomanta ne a lokacin sanyi, ita kuma gwamnati kasafinta na damina ne da rani kan tallafa wa manoma. Duk da sanyin lokacin rani ne, amma ba lokacin ranin da ake noman shinkafa ko wasu abubuwa ba ne. Yana da kyau gwamnati ta yi karatun ta natsu wajen fitowa da tsarin tallafa wa manoman sanyi (ɗari). To wannan noman da ta bari shi ne lokacin da manoma Albasa ke noman ta ba kama hannun yaro, kuma lokacin ne ba a taimaka mana, aka bar mu da dabarar kanmu da kanmu.

Kasuwar albasa

Amma cikin ikon Allah, akwai lokacin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kira ni muka zauna, muka tattauna na yi masa bayani, har yake nuna mana cewa gwamnati ta yi sakaci, ya kuma ba mu tabbacin samar mana da tallafi, amma dai har yanzu shiru saboda kaɗa gangar siyasa da aka yi. Amma yanzu ina neman yanda zan tura masa takarda ne domin neman mu zauna na tunatar da shi kan waccan lamarin, kuma ina da yakinin idan ya tallafa mana ko sau ɗaya ne, to lalle zai yi alfahari damu wajen bunƙasar da tattalin arzikin jihar Sokoto. Domin manoma albasa yan kasuwa ne, nomawa za su yi, kuma siyarwa za su yi su sake noma, haka dai zaa cigaba da tafiya.

Malam Aliyu kamar a ƙalla manomanku na albasa za su kai nawa a Nijeriya?
Eh to, domin samar da sauƙi wajen neman bayani kan noman albasa, mun samar da shafin yanar gizo da jama’a za su iya samun ƙarin haske a kai idan suka je www.noppman.ng. Kuma gabaɗaya masu ci da harkar nan suna kan rijista da ƙungiyarmu.

Ba ku da ƙididdiga ne?
Akwai mana, a Nijeriya muna da manoma albasa sama da miliyan 20, a Sakkwato akwai miliyan biyu.

Kamar da gwamnati za ta ji kiranku, me ku ka fi so a tallafa maku da shi; kuɗi, irin shuka ko mene ne?
Mu manoma Albasa ba ma son a tallafa mana da kudi sam, idan dai za a taimaka mana da iri, magunguna, taki, dama injinan ban ruwa, su ne kaɗai muke so. Kuma duk gwamnatin da ta yi mana haka, ba zamu manta da ita ba.

Mene ne kalamanka na ƙarshe ga manoma da masu kasuwancin Albasa?
To, kirana da manoma kar su yi wasa da kasuwancinsu na noma, su riƙe shi gam, domin kauce wa faɗawa mugun hali ko rayuwa. A daure a cigaba da sana’ar noma. Yanzu ka duba buhun albasa ya kai kusan Naira 20,000. Zuwa sallah za ta iya kai Nara 25,000 zuwa N30,000. Ka dai gani yanzu cikin kasuwar nan kowa hada-hadar albasar ya zo daga lungu da saƙon Najeriya.

Mu na godiya sosai.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *