Sharhi: Yadda ƙasashen yamma suka nuna fuska biyu ga ‘yan gudun hijira

Daga LUBABATU LEI

Jama’a, shin a ganinku akwai bambanci a tsakanin ‘yan gudun hijira?

Bayan ɓarkewar rikicin soja a tsakanin Rasha da Ukraine, dimbin ‘yan gudun hijira sun kwarara daga Ukraine zuwa sauran ƙasashen Turai da ke maƙwabtaka da ita. Ƙididdigar da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta yi ta nuni cewa, ya zuwa ranar 15 ga wata, kusan ‘yan gudun hijira miliyan uku ne suka gudu daga Ukraine, ciki har da dimbin ‘yan ƙasashen Afirka da ke ɗalibta a ƙasar, kuma dan Nijeriya Alexander Orah na daga cikinsu.

Sai dai Alexander Orah ya fuskanci dimbin matsaloli a yayin da ya gudu daga ƙasar. A wani bidiyon da aka wallafa ta kafar sada zumunta, Alexander Orah ya bayyana abin da ya faru gare shi. Da ya isa tashar jiragen ƙasa da ke birnin Kiev,‘yan sanda sun hana shi da abokansa shiga jirgin.

Orah ya ce, “sun ce mata da yara ne kawai aka amince su shiga jirgi, amma ba da jimawa ba, na ga sun kuma hana matan Afirka da na gabas ta tsakiya shiga jirgin, duk da cewa wasunsu suna da ciki.” Bayan fadi tashi da ya yi, daga ƙarshe Orah ya isa kan iyakar Ukraine da Poland. Amma bayan da ya jima yana can, an sanar da shi cewa, “Ya kamata mutanen Indiya da Afirka da ma gabas ta tsakiya su bar wurin, su je kan iyakar Ukraine da Romania.”, a yayin da Orah ya ga yadda fararen fata suka shiga Poland ba tare da wata matsala ba.

A haƙiƙa, abin da ya faru gare shi yana kuma faruwa ga dimbin ‘yan ƙasashen Afirka, da gabas ta tsakiya, da Indiya da ke Ukraine, kuma dalilin faruwar hakan shi ne bambamcin launin fatansu da ƙasashen da suka fito da ma addinansu.

A kwanan baya, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, an nuna bambanci ga ‘yan ƙasarsa da ma na wasu ƙasashen Afirka a kan iyakar Ukraine da wasu ƙasashen Turai. Buhari ya kuma ruwaito labarin da aka bayar da cewa, jami’an ƙasar Poland sun ki amincewa da ‘yan Nijeriya su shiga ƙasar.

Ya ce, sau da dama jami’an ƙasar sun ki amincewa da buƙatunsu, a yayin da wasu‘yan Nijeriya suke neman shiga Poland, abin da ya sa ba yadda za su yi, illa su sake ratsa Ukraine don neman fita daga ƙasar daga kan iyakarta da ƙasar Hungaria.

Buhari ya kuma yi nuni da cewa, “Bisa yarjejeniyar MDD,dukkan mutane na da izini iri daya na shiga wata ƙasa, a yayin da su ke tserewa daga rikici, kuma bai kamata a nuna musu bambanci a sakamakon launin fatansu, ko passport da suke dauke da shi ba.”

Kwatankwacin abin da ya faru ga‘yan ƙasashen Afirka, ƙasashen Turai sun nuna tausayi sosai ga ‘yan gudun hijira na ƙasar Ukraine, waɗanda suka yi ƙoƙarin karɓar su, da ma tsugunar da su yadda ya kamata. Har ma wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labarai na ƙasashen yamma, su na amfani da launin fata a matsayin wata ƙa’ida ta kwatanta ‘yan gudun hijirar Ukraine, da na yankin gabas ta tsakiya da Afrika, inda suke bayar da fifiko ga ‘yan Ukraine din.

Misali, Firaministan Bulgaria, Petkov, ya ce: “wadannan ‘yan gudun hijirar na Ukraine, sun bambanta da mutanen da muka gani a baya. Dukkansu Turawa ne, wadanda su kayi karatu. A baya kuwa, akwai yiwuwar wasu daga cikinsu ‘yan ta’adda ne”. rahoton manema labarai na kafar CBS a Kiev, ya ruwaito su suna cewa, “wannan ba wuri ne da aka shafe gomman shekaru ana ta rikice-rikice kamar Iraƙi ko Afghanistan ba, wannan wuri ne mai wayewar kai, kuma a Turai”.

Wadannan kalamai sun bayyana irin zurfin wariyar launin fata, da fadin rai da suka yi wa Amurka, da sauran ƙasashen yamma katutu. Ashe, a ganinsu, akwai bambanci a tsakanin ‘yan gudun hijira, duk da cewa su ne ƙasashen da suka sha yin kalaman “zaman daidaito a tsakanin ‘yan Adam”, da ma “kare haƙƙin bil Adam”.

A haƙiƙa, ‘yan Adam komai launin fatarsu, da ƙasashen da suka fito, da ma addinansu, rayukansu na da daraja iri daya. ‘Yan gudun hijira ko ‘yan Ukraine ne, ko ‘yan ƙasashen Afirka, da ma na gabas ta tsakiya, abun da ya faru gare su yana baƙanta mana rai, ba tare da wani bambanci ba, kuma ya kamata a samar musu taimako iri ɗaya.