Tashar TRT ta ƙaddamar da sashin Hausa da wasu harsuna uku

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kafar yaɗa labarai ta ƙasar Turkiyya, wato Turke’s Public Broadcaster (TRT), ta ƙaddamar da ƙarin ɓangarori guda uku da za su riƙa yaɗa labarai cikin harshen Hausa da Swahili da Turanci da kuma Faransanci.

Tashar ta TRT ta yaɗa taron masu ruwa da tsaki a harkar na nahiyar Afrika da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Istanbul babban birnin ƙasar Turkiyya.

Tun da farko an ƙaddamar da tashar wacce za ta dinga kawo labarai da rahotanni bisa tsarin dokar yaɗa labarai a gaban mambobin ƙungiyar watsa labarai ta nahiyar Afirka da manyan jami’an gwamnati da kuma jami’an diflomasiyya.

“TRT Afrika za ta kasance kafar yaɗa labarai da za ta dinga bayyana gaskiya da haƙiƙanin zahirin nahiyar Afirka. Wannan dalilin ne ya sa takenmu ya kasance “Afrika a Zahirin Yadda ta ke”, a cewar Darakta Janar na TRT, Mehmet Zahid Sobaci.

Ya ƙara da cewa, kafafen yaɗa labarai na duniya ba sa yaɗa rahotanni masu fa’ida, kyawawan ɗabi’u da al’adun nahiyar Afirka. Sai dai kawai sun ɓige da yaɗa manufofin kafofin yaɗa labarai na yammacin duniya.

“Idan muka kalli Afirka, za mu tabbatar da cewa tana da kyakkyawar makoma,” in ji shi.

Kazalika, ya ce kafar yaɗa labaran za ta zama wata muryar labaran Afirka da ‘yan Afirka a ƙasashen waje, tare da samar da wani dandali na musamman da zai bayyana ainihin ɗabi’un al’ummar nahiyar Afrika a cikin abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.

Sannan ya ƙarkare da cewa, babban burin tashar TRT Afrika da ke da ma’aikata guda 15 daga ƙasashe daban-daban shi ne, samar da ingantattun labarai na musamman tare da yaɗa su cikin fasahar zamani da kuma gabatar da nagartattun shirye-shiryen da suka shafi rayuwar al’ummar Afirka da suke zaune a ko’ina a faɗin duniya da matasa a kafafen sada zumunta na zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *