Tinubu ne kaɗai ya iya tsallake makircin Obasanjo, inji Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ne kaɗai ya tsallake makircin Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo a fagen siyasa.

Buhari ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi game da rayuwar Baba Bisi Akande a otel ɗin Eko kwanan nan a Legas.

A cewar Buhari, “Asiwaju Ahmed Tinubu ya tsallake makircin da gwamnatin Obasanjo ta shirya” a wancan lokaci.

Buhari ya yi wannan furuci ne biyo bayan waiwaye da aka yi dangane da tarihin kafuwar jam’iyyar ‘All Progressive Congress’ (APC) daga jam’iyyar ‘Action congress of Nigeria’ (ACN).

Kazalika, Buhari ya ce makircin Obasanjon bai ƙyale Bisi Akande ba yayin zaɓen jihar Osun a wancan lokaci.

Chief Bisi Akande wanda shi ne Tsohon Gwamnan Jihar Osun 1999–2003, haka nan shi ne shugaban jam’iyyar APC na farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *