Xi ya jaddada buƙatar inganta farfaɗo da yankunan karkara

Daga CMG Hausa

Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jaddada buƙatar inganta farfaɗo da yankunan karkara ta kowacce fuska, da ƙoƙari tukuru domin cimma zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara.

Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin ƙolin JKS, kuma shugaban rundunar sojin ƙasar, ya bayyana haka ne yayin da yake rangadi a birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin ƙasar Sin da birnin Anyang dake lardin Henan, na tsakiyar ƙasar, daga ranar Laraba zuwa yau Juma’a.

Mai fassara: Fa’iza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *