Yaya muka ga babban zaɓen 2023?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Har kullum a kan zuga tsarin dimokraɗiyya da cewa ita ce mafi ingancin hanya ta kawo cigaban ƙasa ta hanyar mutane su zavi wanda su ke so ya jagoarnce su a dukkan matakai. Ba kamar mulkin soja da wasu masu bindiga za su bi dare ko rana ma su ture gwamnati har ma wani lokacin ya kan kai ga zubar da jini ko wulakanta waɗanda su ke kan madafun iko a tsakanin fararen hula. Soja kan yi amfani da bindiga ya harba don ya tsoritar da farar hula ya kwace mulki da ƙarfin tuwo.

Aa na su bangaren fararen hula kan yi amfani da quri’a wajen kawo sauyin da su ke buƙata. Lokacin da Nijeriya ta zauna a ƙarƙashin mulkin sojoji na dogon zamani, fararen hula da dama sun sha azaba ko gallazawa daga sojojin a duk lokacin da su ka yi yunqurin a dawo da mulki hannun farar hula don wakiltar ra’ayin al’ummar ƙasa. Wasu ’yan gwagwarmayar kan rasa ran su wasu kuma a tura su gidan yari. Duk da an samu Nijeriya ta dawo mulkin farar hula a 1999 amma wani abun dubawa sojojin masu bindiga a jiya da ba sa haɗa inuwa ɗaya da farar hula su ne su ka rikiɗe su ka koma farar hula kuma ba sa shayin cewa su sojoji ne a baya.

Da son samu ne asalin ’yan siyasa su jagoranci gwamnatin siyasa don tunanin asalin ɗan siyasa na da bambanci da irin aƙidar da soja ya zauna a kai har tsarin ya yi kan ta a jikinsa cewa farar hula ba komai ba ne kuma in ya yi laifi a ba shi kashi ne hanyar ladabtarwa. Duk daɗewar soja da yin ritaya wataran sai ka ga ya tashi ya na sambatun tuna yaƙi ko neman ɗaukar bindiga da makamantansu. Wani lokaci ka ji soja na cewa ya sha kwaramniyar yaqin basasa ya yi kaza ya yi kaza. Tsarin soja da farar hula zalla akwai bambancin kamar hanyar jirgi daban hanyar mota daban.

In an duba yanzu an caquda mutanen biyu su na zaune a ɗaki ɗaya da yunƙurin sai sun zama kan tsari ɗaya. Wannan yunƙurin ba zai iya nasara ba don kowa gidan su daban. Kama daga tsarin tattalin arziki, samar da ayyukan yi, lamuran tsaro, haɗin kan qasa, girmama tsarin marigaya da su ka yi gwagwarmayar karvo ‘yancin ƙasa da sauran su sai an samu bambancin tunani na fitar hankali tsakanin bagwaren ɗan siyasa mai bindiga da ɗan siyasa sadidan mai tasbaha a hannu ko sarka mai gicciye a wuya.

Tsarin tinkarar matsalolin ƙasa da girmama shawara ko tunanin ’yan ƙasa ya kan samu cikas ko karɓuwa bisa irin tarbiyyar da masu riƙe da mukaman siyasa su ka tashi a kai. Wani shugaban siyasar zai yi kememe ya na shiru alhali ga jama’a na ba da shawara mai ma’ana.

Za ka ga a na ta magana har a kafafen labaru kan yadda ya kamata a aikata wani aiki ko a hau kan wani tsarin da zai taimaki ƙasa, sai shugaba ya yi biris da wannan don a wajen sa masu maganar ba su kai su yi magana ba ko kuma ko sun yi maganar ba ta da amfani don tamkar ba su da kwarewa ko ƙarfin maganar ko ma hurumin magana, kawai matsayin su na ’yan a bi Yarima a sha ƙida ne kawai.

Duk yadda mutum zai so ƙasa ta cigaba sai ya samu haɗin kan shugabannin ƙasar kama daga fadar gwamnati, majalisar dokoki har ma da tabbatar da a na hukunci mai adalci a kotuna. Duk turken da ya ke da matsala a tsakanin su zai kawo tangarɗa. Ai kamar duwatsun murhu ne guda uku ne ba kamar teburi mai kafa huɗu ba.

Akwai lokacin da a ka samu shugaban ƙasa tsohon soja shugaban majalisar dattawa ma tsohon soja kuma ga tsoiffin sojoji da dama a manyan muƙamai a gwamnatin da kuma kasancewa a cikin majalisar dattawa. Ga sojoji nan ba kayan sarki su na mulkin ƙasa. A wani lokacin kuma za a samu farar hula gaba da baya amma mai bussasshiyar zuciya ko ya zama cike da son kai don haka ba zai yi abun da zai inganta rayuwar jama’a ba.

Shi ya sa in ka ga gwamnati na mulkin ko oho ko na kama karya to ka duba asalin mai mulkin sai kuma ka dawo kawaziransa musamman waɗanda ke kewaye da shi kullum a fadarsa. Duk rashin jin maganar mai mulki idan ya na samun shawarar da ta dace daga ’yan fadarsa to za a iya samun dama-dama ko da babu gara ba daɗi.

Ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓen shugaban Nijeriya na shekara ta 2023 da a ka fafata tsakanin jam’iyyu 18.

Tinubun dai ya lashe ne don yawan ƙuri’a amma sauran abokan takarar ta sa Atiku na PDP da Peter Obi na Leba aƙalla sun tagaza a kashi 25 na yawan ƙuri’a a 2/3 na yawan jihohin Nijeriya.

Shugaban hukumar zaɓen Farfesa Mahmud Yakubu ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaven da samun sama da ƙuri’a miliyan 8.8 inda ya ɗara mabiyinsa a yawan ƙuri’a Atiku Abubakar da ke da sama da ƙuri’a miliyan 6.9. Peter Obi na jam’iyyar Leba ke zama na uku da yawan ƙuri’a sama da miliayn 6. Wani abun dace duk manyan ’yan takarar uku sun yi galabar a yawan ƙuri’a a jihohi 12 kowanne inda Rabi’u Kwankwaso na NNPP ke zama na huɗu da galabar a jihar Kano.

Bai zama abun mamaki ba a ce Tiunbu ya yi nasara a jihohin yarbawa, ko Atiku ya samu nasarar da ya sake samu yanzu, amma yadda Peter Obi ya girgiza zaɓen da samun mara baya a jihohin kudu maso gabar da kudu maso kudu da lashe jiharsa da gagrumin rinjaye duk da rashin jituwarsa da gwamna Charles Soludo ya zama abun mamaki ko darashin tattaunawa.

Tuni ’yan APC su ka hargitse da murnar samun wannan nasara da nuna kwarin gwiwar shugaban mai jiran gado ba zai nuna bambanci a mulkinsa tsakanin dukkan sassan Nijeriya ba. Gabanin nan, manyan jam’iyyun adawa da su ka haɗa da PDP da Leba sun yi watsi da sakamakon da buƙatar a soke zaɓen.

Za a jira a ga yadda lamura za su cigaba da kasancewa har zuwa ranar 29 ga watan mayu yayin da shugaba Buhari zai sauka daga mulki a rantsar da sabon shugaba.

Manyan jam’iyyun hamayyar Nijeriya sun yi taro na musamman inda su ka ayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da a ka gudanar ranar asabar ɗin makon jiya.

Jam’iyyun sun buƙaci a soke zaɓen da nuna tamkar an kwari ‘yan qasa kan ɗawaniyar kaɗa ƙuri’a ba tare da samun biyan buƙata ba.

Taron ya gudana ne gabanin ayyana sakamakon zaɓen da dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a matsayin wanda ya lashe.

Duk da jam’iyyun kai tsaye ba su faɗi abun da za su yi ba in ba a soke zaven ba, amma da alamu za su ƙalubalanci sakamakon a kotu.

Kan gaba a jam’iyyun akwai babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma Leba ta ƙungiyar ƙwadago waɗanda har ila yau su ke kan gaba a samun ƙuri’a bayan jam’iyyar APC.

Kiraye-kirayen amincewa da ƙaddara da kuma bitar zaɓe sun fara fitowa;

A gefe guda dattawan ƙasa sun rabu gida biyu tsakanin masu buƙatar a ɗauki ƙaddara wajen amincewa da sakamakon zaɓen da kuma masu cewa a gudanar da bincike.

Babban abun da masu buƙatar a amince da sakamako ke cewa shi ne ko yaya a ka yi mutum ɗaya kan lashe zave kuma duk wani ƙoƙari na ƙalubalantar sakamakon zai iya haifar da fitina a ƙasa.

Masu neman a yi bincike na ganin hukumar zaɓe ba ta cika alƙawarin fito da sakamakon da ke kan na’urarar hana maguɗin zaɓe ta BVAS wacce hukumar ke tutiyar cewa za ta bayyana sakamako da na’urar tare da sakamakon kan takarda.

Hukumar zaɓen dai a kai tsaye ba ta bayyana dalilin rashin fito da sakamakon BVAS ba inda ta cigaba da nuna sakamakon kan takarda da ba da umurnin a gyara wasu alkaluman tuntuɓen rubutu ko harshe daga jami’an gabatar da sakamako.

Duk da haka su kuma ƙananan jam’iyyun adawa da su ka amince da yadda a ka gudanar da bayyana sakamakon na cewa ko wace jam’iyya na da wakili a rumfar zave, don haka wanda bai gamsu da rahoton da wakilinsa ya kawo ba ko ya ji bai gamsu da abun da a ka yi ba, sai ya garzaya kotu.

Kammalawa;

Komai ya yi farko zai yi ƙarshe ban da ikon Allah. Hatta wannan zaɓen da a ka yi idan an rantsar da Tinubu to wataran a kwana a tashi in da nisan kwana za a ji a na saura kwana kaza ya sauka daga mulki bisa tanadin tsarin mulki.

Kamar misalign shugaba Buhari ne da talakawa su ka share shekaru su na fafutukar ya samu karagar mulki, to ga shi ƙarshe ya samu har ma saura ƙasa da wata 3 ya sauka! Mu maida lamari ga Allah don samun jagorar Maɗaukakin Sarki.
Nijeriya.