Daga CMG HAUSA
A ranar Laraba ne hukumar MDD mai lura da ‘yan gudun hijira, ta bayyana cewa, sama da ‘yan ƙasar Ukraine miliyan 5 ne suka kwarara zuwa ƙasashen Turai makwafta, lamarin da ya haifar da gagarumar matsalar ‘yan gudun hijira.
To sai dai kuma, yayin da wasu sassan ke ganin nahiyar Turai ce mafi tafka asara, tun bayan ɓarkewar rikicin Rasha da Ukraine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce tun bayan ɓarkewar rikicin watanni 2 da suka gabata, a yanzu duniya na kara fahimtar ɓangaren da ke more riba, sakamakon rikicin.
Zhao wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya ce duk da Amurka na yiwa kan ta kirarin mai kare haƙƙoƙin bil adama, a hannu guda, ‘yan ƙasar Ukraine 12 ne kacal suka samu mafaka a Amurka cikin watan Maris da ya shuɗe, ƙarƙashin shirin ta na baiwa ‘yan gudun hijira matsuguni.
Game da kalaman wasu ‘yan siyasar Amurka, na zargin ƙasar Sin da karya ƙa’ida kuwa, Zhao Lijian ya ce, babu wata ƙasa da ta kai Amurka ƙalubalantar, da ƙoƙarin lalata tsarin dokokin kasa da ƙasa, da ma duk wani tsari na cuɗanyar ƙasashen duniya.
Mai fassarawa: Saminu