Editor

9513 Posts
 Ilimin boko ma wani ɓangare ne na taimakon Muslunci da al’ummar musulmi

 Ilimin boko ma wani ɓangare ne na taimakon Muslunci da al’ummar musulmi

ABDULAZIZ TIJJANI BAKO (PhD) Umurni na farko da Allah (SWT) ya bai wa Annabi (S.A.W) a Kurani shi ne ya yi karatu (Ikra' bismi rabbikalladhi khalak: Yi Karatu! Da sunan Ubangijinka, wanda Ya halicci komai da komai). Wannan aya karara ta nuna cewa daya daga cikin abinda ya fi komai muhimmanci ga rayuwar dan’adam shi ne ilimi. A inda mishkilar take shi ne sau da yawa mutane suna dauka cewa a musulunci idan ana maganar ilimi, kawai zallan ilimin addini a ake magana, wanda hakan kuma kuntata fahimta ne. Ko shakka babu idan ana maganar ilimi a addinin musulunci ana…
Read More
Bincike: EFCC ta ƙwace fasfo ɗin Betta da Sadiya

Bincike: EFCC ta ƙwace fasfo ɗin Betta da Sadiya

A ci gaba da gudanar da bincike da take yi kan zargin almundahana, Hukumar Yaki da Rasahawa ta EFCC, ta kwace fasfo din dakatacciyar Ministar Jinkai da Yaki Talauci, Betta Edu da na wadda ta gada, Sadiya Umar-Farouq. Ya zuwa hada wannan rahoto, Betta na hannun EFCC na ci gaba da amsa tambayoyi tun bayan da ta kai kanta ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Talata da misalin karfe 10 na safe. Bayanai sun ce binciken zargin wawushe Naira biliyan 44 da ake yi wa Betta ya hada har da wasu majojin bankuna su uku wanda su ma suka…
Read More
Cin zarafi a aure:  Ina mafita?

Cin zarafi a aure:  Ina mafita?

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a kasar Hausa. Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran hakkokinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulakanci. Amma ta kafe ta hakura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma meye mafita? Yawanci sukan dauki matakin hadiye komai su cigaba da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya buƙaci Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa da ta kammala aikin titin Katsina zuwa Kano

Gwamna Raɗɗa ya buƙaci Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa da ta kammala aikin titin Katsina zuwa Kano

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, yayi wannan roko ne a lokacin da ya kai ziyara a ofishin Ministan Ma’aikatar Ayyuka, Sanata David Umahi, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu 2023 a Abuja. A lokacin ziyarar, Gwamnan ya samu rakiyar Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Katsina, Injiniya Sani Magaji, Alh Abdullahi Turaji da sauran su. Gwamna Radda ya jaddada wannan bukatar ne, inda ya yi nuni da cewa, duk da cewa an bayar da kwangilar gina hanyar a shekarar 2019, amma aikin nayin tafiyar hawainiya. Ya kuma bayyana muhimmancin sa hannun gwamnati bisa la’akari da…
Read More
Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (III)

Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (III)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A makon jiya muka cigaba da kawo wa masu karatu takaitaccen tarihin sarakunan Fulani wadanda suka fara mulkin kasar Kano tun daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo kawo yau. To, a yau za mu cigaba gaba inda muka tsaya. A zamanin Sarki Alu an samu sa-in-sa a tsakanin Ningi da Kano. Amma saboda Sarki Danyaya yana jin tsoron Sarki Alu sai ya zama ba a gwabza yaki ba. Sannan dai a zamanin Sarki Alu ne gaba ta tsananta a tsakanin Kano da Hadeja. A wannan zamani Sarki Muhammadu ne ya ke sarautar Hadeja. Sarkin Kano Alu…
Read More
Gwamna Lawal ya raba wa manoma kayan aiki a shiyyar  Zamfara ta Arewa

Gwamna Lawal ya raba wa manoma kayan aiki a shiyyar  Zamfara ta Arewa

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ci gaba da aiwtar da shirinsa na raba wa manoman jihar kayayyakin aikin gona inda a wannan karon shirin ya yada zango a shiyyar Zamfara ta Arewa. A ranar Alhamis ta makon jiya aka kaddamar da rabon kayayyakin a Gidan Gona da ke yankin Karamar Hukumar Shinkafi. Rabon kayayyakin in ji Mai magana da yawunsa, bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi wajen tada komadar tattalin arziki bayan wucewar annobar Korona. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa za a kaddamar da…
Read More
Gwamnan Zamfara ya sha alwashin  ɗabbaƙa kasafin 2024

Gwamnan Zamfara ya sha alwashin  ɗabbaƙa kasafin 2024

Gwamnan Jihar Zamfara,  Dauda Lawal, ya sha alwashin aiwatar da kasafin gwamnatinsa a 2024 don amfanin jihar da al’ummarta. Lawal ya sha alwashin haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron Majalisar Zartarwa da ya gudana ranar Litinin karkashin jagorancinsa a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar. Mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa, taron majalisar ya tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jihar, ciki har da batun kasafin jihar na 2024. Sa’ilin da yake jawabi, Gwamna Lawal, ya jaddada zai yi amfani da ingantattun tsare-tsaren da ke kunshe cikin kasafin…
Read More
Aure ya yi albarka: Darakta Kamal S. Alƙali da Jaruma Hauwa S. Garba sun samu ƙaruwa

Aure ya yi albarka: Darakta Kamal S. Alƙali da Jaruma Hauwa S. Garba sun samu ƙaruwa

DAGA MUKHTAR YAKUBU. Darakta Kamal S. Alkali da amaryar sa Jaruma Hauwa S. Garba sun samu karuwar haihuwar da namiji wanda aka radawa suna Ahmad. A ranar 23 ga Disambar shekarar da ta gabata 2023 ne aka yi haihuwar a wani asibiti mai zaman kansa a cikin garin Kano. Cikin murna da jin dadi, Kamal S Alkali, ya bayyana godiyar sa ga Allah da ya nuna masa wannan lokaci da matar sa Hauwa S Garba ta yi wannan haihuwar bayan wata 10 da auren su. Domin kuwa an daura masu aure ne a watan Maris din da ya gabata wanda…
Read More
Yadda sabon bidiyon waƙar ‘Tarko’ ke haskawa a Masana’antar Kannywood

Yadda sabon bidiyon waƙar ‘Tarko’ ke haskawa a Masana’antar Kannywood

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Kamfanin Bee Safana production Place ya fito da wani sabon Bidiyon waka mai suna 'Tarko', wanda fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Daddy Hikima (Abale) da fitacciyar jaruma mai haskawa Bilkisu Bee Safana suka fito a ciki. Wakar wacce ta fito da sabon salo mai ban sha'awa ta samu karbuwa kuma tana kan samu a daidai wannan lokaci. Bidiyon wakar ya nuna yadda wani azzalumin shugaba ke kama wata budurwa (Bee Safana) ya daddaureta da igiya yayin da shi kuma masoyinta (Abale) ya ke zuwa yana arangama da wadannan mutanen don ganin ya kwato masoyiyar tasa, amma…
Read More
An ɗaura auren jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz, a Maiduguri

An ɗaura auren jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz, a Maiduguri

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A yanzu haka dai ta tabbata jarumin Kannywood Abdullahi Amdaz ya zama mai igiya biyu. Amdaz ya kara aure a ranar Asabar, 30 ga Disamba, 2023 a garin Maiduguri, Jihar Barno An daura auren Abdullahi Amdaz da abar kaunar sa A'isha Umar Timta da misalin karfe 11:00 na safe a gidan sarkin Gwoza da ke kan Titin Gombale, kusa da makarantar Capital, Giwa Barrack, Maiduguri, Jihar Barno. Allah ya ba su zaman lafiya da zuria dayyiba.
Read More