Editor

9513 Posts
Tinubu ya tsige manyan jami’an gwamnati guda biyu

Tinubu ya tsige manyan jami’an gwamnati guda biyu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tsige Mataimakin Shugaban  hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki da aka fi sani da FCCPC a takaice, Mr. Babatunde Irukera. Kazalika, Tinubu ya tsige Babban Daraktan Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Mr. Alexander Okoh. Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Chief Ajuri Ngelale ne ya bayyana tsigewar cikin sanarwar da ya fitar  jiya Litinin, inda ya ce matakin tigewar ya fara aiki ne nan take. Sanarwar ta kara da cewa, an umarci jami’an da lamarin ya shafa da su mika ragamar gudanar da ofisoshinsu ga jami’i mafi girma a bakin aiki a ma’aikatarsu…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Dandalin shawara: Mijina ya nisanta kansa da zama uban cikin da ke jikina

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Aisha Asas barkanki da yau. Ya jama'a dai. To madalla. Don Allah ki taimaka min yadda ki ka saba ba wa mutane shawara da suke amfana da ita har ta yi masu aiki ga abinda yake ta damun rayuwarsu. Kina ji na ko, wato miji ne nake tare da shi da ban san kowanne irin mutum ne ba, ya sani duk daren Allah sai ya………..(mun cire kalmomin saboda rashin dacewar ta). Kuma kar ki ce sau daya, har ba iyaka. To wai yanzu na yi ciki, asibiti an ce Ina dauke da juna biyu na wata…
Read More
Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarni kan a dakatar da Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu daga mukaminta na minista. Kuma dakatarwar ta fara aiki ne nan take, kamar yadda Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Betta ne domin kare mutuncin gwamnatin kasa da kuma aiki da gaskiya. Ta kara da cewa, Tinubu ya bai wa Shugaban EFCC umarni kan gudanar da cikakken bincike a kan Betta bisa zargin da ake yi mata na karkatar da wasu makudan…
Read More
Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Kafafen Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ta bayyana cewa akwai yiwuwar masu amfani da layin sadarwa na kamfanin Globacom su fuskanci kwarya-kwaryar dakikewa wajen kiran layukan sadarwa na kamfanin MTN. Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ran Litinin wadda ta samu sa hannun Daraktan Sashen Hulda da Jama'a, Reuben Muoka. NCC ta ce za a fuskanci hakan ne biyo bayan rashin biyan harajin sadarwa daga bagaren Globacom. Hukumar ta kara da cewa ta ba da izinin a katse sadarwar kamfanin Globacom daga MTN Nigeria Communications Plc. A cewar Hukumar, “An sanar…
Read More
Hajjin 2024: Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna

Hajjin 2024: Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna

Daga BASHIR ISAH An cimma yarjejeniyar aikin Hajjin bana tsakanin Gwamnatin Nijeriya da takwararta ta kasar Saudiyya. A ranar Lahadin da ta gabata bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Jedda, kasar Saudiyya, inda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya wakilci Gwamnatin Nijeriya. Yayin wani taron ban gishiri, in ba ka manda da suka yi tare da Ministan Hajji da Umarah na Saudiyya, Dokta Taofiq bin Fawzan AlRabiah, Tuggar ya bayyana cewa ayyukan Hajjin 2024 za su gudana ne bisa sabbin dokokin da aka gindaya domin tabbatar da komai ya gudana a kan lokaci. Tattaunawar tasu…
Read More
Shin kashe Al-Arouri ya kashe Hamas?

Shin kashe Al-Arouri ya kashe Hamas?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Duk wani yaki na bukatar manyan dakaru da kan zama ginshikai kuma a ke daukar wa imma umurni daga wajen su ko koyi da irin jarumtakarsu. Mun dai san cewa tun watan Oktobar bara a ke gwabzawa tsakanin Isra’ila da kungiyar HAMAS ta Falasdinawa da ke jagorantar yankin Gaza. Yakin dai tamkar tsakanin mai jifa da dutse ne da mai zarerren takobi ko ma fiye da haka na makaman gayawa jini na wuce. Sojojin Isra’ila na amfani da jiragen yaki, tankunan yaki da manyan bindigogi kan ’yan HAMAS. Su kuma ’yan HAMAS na cilla rokoki…
Read More
Abin da ’yan Nijeriya ke buƙata a 2024

Abin da ’yan Nijeriya ke buƙata a 2024

Shekarar da ta gabata, 2023, shekara ce da ta zo da kalubale ga 'yan Nijeriya. Ta zo ne da zazzabin gabatowar babban zaben 2023 tare da zuwa karshe da munanan hare-haren ta'addanci a Jihar Filato a lokacin Kirsimeti. Dangane da wahalhalun tattalin arziki da ya biyo bayan matakin farko na tattalin arziki na sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, gwamnatin ta yi bayanin cewa hakan ne farkon kuma karshen zafin rayuwa ga 'yan kasa a cikin sabon tsarin fatan shugaba Tinubu. Sai dai kuma a wannan shekara ta 2024 akwai wasu abubuwa da ’yan Nijeriya ke son ganin sun faru a…
Read More
Sana’a da arziki a ma’aunin hankali suna da alaƙa ta ƙud da ƙud – Kamal

Sana’a da arziki a ma’aunin hankali suna da alaƙa ta ƙud da ƙud – Kamal

Daga AMINA YUSUF ALI Kamal Alkasim wani masani ne a fannin kasuwanci da tattalin arziki wanda ya gogu a harkar. Ga wasu shawarwari da ya bai wa masu sana'a don inganta rayuwarsu ta fannin tattalin arziki: A wannan lokacin da yawan masu sana'a kama ya yi su kara wa sana'o'insu kishiyoyi , wannan kuma ba shi da ita ya rungume ta domin ita ce silar samun arziki tilo. Duk arziki yana kunshe cikin sana'a domin ita ce hanya ingantacciya ta samunsa. Rungumar sana'o'i kanana da matsakaita ga matasanmu wannan zai zama kamar juyin juya halin yaqar talauci a wannan lokaci…
Read More
Airtel Afirka ta yi sabon shugaba

Airtel Afirka ta yi sabon shugaba

 Daga AMINA YUSUF ALI Airtel Afirka ta ba da sanarwar ritayar  Babban Jami'in Zartaswarsa, Olusegun Ogunsanya, wanda zai akiye aiki a ranar 1 ga Yuli, 2024. Ogunsanya, ya fara aiki da kamfanin  Airtel a shekarar  2012, shi yake kula da harkokin sadarwa na Nijeriya da kamfanin hada-hadar kudi na tsahon shekaru tara kafin a yi masa nadin  Babban Jami'in Zartaswar rukunin kamfanonin a cikin shekarar 2021. Saboda saninsa da yadda Afirka take da gidewarsa waen rarraba kaya a cikinta, ya kasance a lokacin da yake shugabantar kamfanin ya samar da bunkasar kudin shiga masu tarin yawa tsahon shekaru, sannan ya…
Read More
Tsaro: Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher

Tsaro: Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher

Daga BASHIR ISAH Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, dangane da kokarin da yake yi wajen kare rayukan ‘yan kasa da kuma dukiyar gwamnati. Matasan sun yi wannan yabo ne ta bakin kungiyarsu ta Northern Youths Association of Nigeria (NYAN) cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar ranar Asabar a Bauchi. Matasan sun ce, “Mun yaba da kokari da jajircewarsa wajen maido da zaman lafiya a Nijeriya. Hakika ya dora rundunar sojin Nijeriya kan turbar da ta dace. Shugaban kungiyar,  Ambasada Godiya T. Adams Bogoro, ya bayyana cewa, bayan nazari da lura,…
Read More