Editor

9513 Posts
Rubutuna ya fi mayar da hankali kan illolin bin bokaye da ‘yan tsubbu – Lailat Abdullahi

Rubutuna ya fi mayar da hankali kan illolin bin bokaye da ‘yan tsubbu – Lailat Abdullahi

"Ya kamata manyan marubuta su kama hannun ƙanana, su yi masu jagora" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Zainab Abdullahi Musa mai laqabi da Lailat, matashiyar marubuciya ce daga Jihar Katsina, wacce ta kasance mai himma da kishin rubutun adabin Hausa. Duk da kasancewarta ɗalibar koyon aikin jinya, bai hana ta ware lokaci na musamman don yin rubutun da zai taimaka wajen ilimantar da matasa ƴan'uwanta game zamantakewar rayuwa, da muhimmancin bin iyaye. Kawo yanzu ta rubuta littattafai guda biyar, har yanzu tana cigaba da rubutu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, marubuciyar ta bayyana masa irin gwagwarmayar da ta sha kafin…
Read More
An garzaya da shugaban NLC asibiti bayan gana masa baƙar azaba

An garzaya da shugaban NLC asibiti bayan gana masa baƙar azaba

Daga BASHIR ISAH An garzaya da shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Comrade Joe Ajaero, zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Owerri sakamakon baƙar azabar da ya sha a hannun 'yan sanda. An garzaya da Ajaero asibitin ne alhali idonsa na dama a kumbure suntum. Shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa a jama'a na NLC, Benson Upah, ya bayyana lamarin da yunƙuri garkuwa wanda ya riƙiɗe ya zama yunƙurin kisa. A cewar Upah, “An gayyaci Joe Ajaero da misalin ƙarfe 15:30 a asibitin'yan sanda da ke Owerri, daga nan kuma aka ɗauke shi zuwa Babban Asibitin Tarayya a Owerri…
Read More
Rayuwar ‘yan matan Arewa a Tiktok

Rayuwar ‘yan matan Arewa a Tiktok

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na daɗe ina son na yi wannan rubutun domin jan hankali da faɗakarwa ga al'ummarmu ta Arewa musamman iyaye da ’yan mata game da wasu abubuwa da ke faruwa, amma wasu dalilai suna sa ina jinkirtawa, sai a wannan karon da batun wata yarinya mai suna Rahama Sa'idu da ta yi karatu a Kwalejin Koyar da Aikin Jinya ta Jihar Kebbi ya taso, inda rahotanni ke cewa wai hukumar gudanarwar makarantar ta kore ta saboda rashin mayar da kai a karatu da sharholiyar da aka ce tana yi a manhajar Tiktok. Kodayake wata majiya ta…
Read More
Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (1)

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (1)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya, wanda ya rubuta fiye da littattafai (400) na addinin Musulunci da hannunsa. Malamin, wadda jigo ne a ɗarikar Tijjaniyya a halin yanzu shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Fatawa da Al'amuran Musulunci a Nijeriya (NSCIA). Malamin ya kasance ɗan ƙabilar Shuwa Arab, kuma ya yi karatu a wurare da dama da suka haɗa da; Makka, da Madina, da Masar, da Pakistan, da Iran, Senegal da sauran su, a wajen manyan malaman Musulunci, ciki har da babban makarancin Al-Ƙur'anin nan Mahmoud Khalilul Khusari, a Masar. An haifi Sheikh Sharif Ibrahim Saleh…
Read More
Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A wannan mako zan so na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta bayan rabuwar aurensu. Da farko dai wacece bazawara? Bazawara ita ce wacce ta rabu da mijinta ta hanyar sakin aure ko kuma wanda ya mutu, ko ma wanda ya vace. Ƙasar Hausa kamar yadda muke gani a halin yanzu, ta zama tamkar shalkwatar yaye ƙanana da manyan zawarawa har ma da dattijai. Ba sai na kawo dalilan da suke…
Read More
Abin da ya sa ban damu da saka fitattun jarumai a finafinaina ba – Kabiru Musa Jammaje

Abin da ya sa ban damu da saka fitattun jarumai a finafinaina ba – Kabiru Musa Jammaje

DAGA MUKHTAR YAKUBU Bayan tsawon lokacin da ya shafe ba tare da ya fito da sabon fim ba, fitaccen furodusa Kabiru Musa Jammaje, wanda ya saba shirya finafinai da harshen Turanci a masana'antar Kannywood. A yanzu haka dai ya ci gaba da shirya sabon fim ɗin sa mai suna 'Princess of Galma,'. Wakilinmu ya tattauna da shi a game da yadda aikin fim ɗin yake da kuma manufarsa ta shirya wannan sabon fim ɗin, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance MANHAJA: Kai ba sabo ba ne a cikin harkar fim a wannan masana'anta ta…
Read More
Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na takwas

Messi ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na takwas

Lionel Messi ya lashe kyutar gwarzon ɗan kwallon ƙafa na duniya na 2023, Ballon d'Or. Wannan shi ne karo na takwas da Messi ke lashe wannan kyauta ta bajinta a duniyar wasan tamaula. Messi tsohon ɗan wasan Barcelona da Paris St Germain mai taka leda a Inter Miami a Amurka ya ɗauki kofin duniya a Qatar a 2022. Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe babban kofin duniya na farko a wajensa, sannan na uku a kasar jimilla.
Read More
Ƙungiyar ‘Neighborhood Development Associantion’ ta gudanar da ayyukan cigaban al’umma

Ƙungiyar ‘Neighborhood Development Associantion’ ta gudanar da ayyukan cigaban al’umma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A cigaba da gudanar da muradun da suka assata, Ƙungiyar 'Kwanar Bushara Neighborhood Development Associantion' da ke Unguwar Rigasa ta Jihar Kaduna ta gudanar ayyukan gyaran tituna domin jin daɗin jama'a. Ƙungiyar ta kwashe makonni biyu tana fitowa duk ranar Lahadi domin cike ramukan da suka addabi direbobi da sauran jama'a a kan babban titin Maƙarfi Road, inda suka rinqa bi suna cike manyan ramuka da ƙanana. Wakilinmu da ya shaidi wannan aiki ya shaida mana cewa, mambobin ƙungiyar sanye da rigunan da ake alamta su ne suka rinƙa bi suna haƙewa tare da cike ramukan…
Read More
Malaman addini sun zama mabarata a gaban ‘yan siyasa – Rafsanjani

Malaman addini sun zama mabarata a gaban ‘yan siyasa – Rafsanjani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Darakta na Cibiyar Bayar da Shawara ta 'Civil Society Legislative Advocacy Centre' (CISLAC) Auwal Rafsanjani, ya ce galibin malaman addini da ke zuwa bara wajen shugabannin siyasa su na zubar da mutuncin su. Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a wani shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, Rafsanjani ya ce, al’ummomi da shugabannin addinai da ya kamata su tabbatar da adalci da zama ginshiƙin gaskiya a cikin al’umma sun zama ‘mabarata’ ga ’yan siyasa. Ya ce, “A da, mun san yadda kakanninmu suka tsaya ga…
Read More
Zuwa ga mata…

Zuwa ga mata…

Tsawon zamani, wasu ba su ɗauki ‘mace mutum ba’ saboda ta kasance mai rauni ta yadda ake mata kallon ba za ta iya komai ba sai dai kula da yara da kuma aikace-aikacen gida da dai sauransu. Akan tauye mata haƙƙin neman ilimi ko kuma bada wata gudunmuwa don cigaban al’umma tare da mayar da ita tamkar baiwa. A mahangar addinin Musulunci, mace tana da kima sosai, sannan kuma tana da cikakken ’yancin yin duk wani abu da bai sava wa koyarwar addini ba, kama daga kasuwanci, neman ilimi da sauransu. Amma duk da wannan damar da addini ya ba…
Read More