Editor

9513 Posts
Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Kano karkashin jagorancin Alkali Usman Na’abba, ta yan ke wa wanda ya kitsa sacewa da kashe Hanifa Abubakar 'yar shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya. A ranar Alhamis kotun ta yanke wannan hukunci, inda ta ce dole Tanko ya bakunci lahira bayan kama shi da laifin kisa. Tanko shi ne mai makarantar Nobel Kids Academy inda nan marigayiya Hanifa ke tafiya kafin cimma ajalinta. Idan dai za a iya tunawa, a ranar 4 ga Disamban 2021 aka yi garkuwa da Hanifa a kan hanyarta ta komawa gida daga Islamiyya, inda…
Read More
Za mu ceto Zamfara, inji Atiku yayin da ya amshi baƙuncin Dauda Lawal

Za mu ceto Zamfara, inji Atiku yayin da ya amshi baƙuncin Dauda Lawal

Daga WAKILINMU Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya jaddadawa Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal cewa zai yi aiki tuƙuru wurin ganin jam'iyyar PDP ta lashe zaɓen 2023 a Jihar da ma ƙasa bakidaya. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana haka ne jiya laraba a gidansa dake Abuja, yayin da Dauda Lawal ya jagoranci tawagar 'ya'yan PDP na Jihar Zamfara tare da wasu jiga-jigan 'yan siyasa da suka sauka sheƙa daga APC zuwa PDP. Atiku ya ce, hanya daya ce za a iya bi wurin ceto Zamfara, shi…
Read More
Duk lokacin da na fitar da sabon littafi na kan kashe wayata na ɗan lokaci – Zainab Birget

Duk lokacin da na fitar da sabon littafi na kan kashe wayata na ɗan lokaci – Zainab Birget

"Ba zan bar rubutu ba har sai idan shine ya bar ni"Daga MUkHTAR YAkUBU a Kano Zainab Lawan Birget tana ɗaya daga cikin fitattun mata marubuta da suka ɗauki lokaci mai tsawo a cikin harkar, domin kuwa ta shafe sama da shekaru 20 tana yin rubutun wanda kuma a tsawon lokacin da ta shafe ta rubuta littattafai masu yawan gaske. Ganin yadda harkar rubutun ta koma a yanzu a matsayinta ta tsohuwar marubuciya, mu ka nemi jin ta bakinta a game da irin hangen ta a kan makomar rubutu da kuma littattafai a yanzu da kuma nan gaba. Ku biyo…
Read More
Ƙasar da ke haifar da tashin hankali a duniya

Ƙasar da ke haifar da tashin hankali a duniya

Daga LUBABATU LEI Wani nazarin da cibiyar nazari ta Cato ta ruwaito a watan Afrilun bana ya yi nuni da cewa, cikin shekaru biyun da suka gabata, a ƙalla jami’an soja da suka samu horo daga Amurka sun tsara juyin mulki har sau huɗu, daya a shekarar da muke ciki a ƙasar Burkina Faso, daya a bara a ƙasar Guinea, sauran biyun kuma a ƙasar Mali. Baya ga haka, ƙididdigar da aka fitar ta yi nuni da cewa, daga farkon ƙarni na 20, Amurka ta kuma tsara gomman juye-juyen mulki a ƙasashen Latin Amurka. Haƙiƙa, yadda Amurka ta sha kitsa…
Read More
Ribar masana’antun Sin ta ƙaru da kaso ɗaya bisa ɗari a rabin farko na bana

Ribar masana’antun Sin ta ƙaru da kaso ɗaya bisa ɗari a rabin farko na bana

Daga CMG HAUSA Ribar manyan masana’antun ƙasar Sin ta ƙaru da kaso ɗaya bisa ɗari a rabin farko na shekarar bana, kamar yadda alƙaluman kididdiga da aka fitar a yau Laraba suka tabbatar da hakan. Babban jami’i a hukumar ƙididdigar ƙasar NBS Zhu Hong, ya alaƙanta wannan ci gaba, da matakan aiwatar da cikakkun tsarukan shawo kan annobar COVID-19, da na raya tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma matakai daban daban da aka aiwatar, domin saita akalar tattalin arzikin ƙasar. Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa
Read More
Ƙasashen Afirka suna da hikimar zaɓen abokan haɗin gwiwa da kansu

Ƙasashen Afirka suna da hikimar zaɓen abokan haɗin gwiwa da kansu

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Afirka ita ce Afirka ta jama’ar Afirka, kuma ƙasashen Afirka tana da hikima da sanin ya kamata wajen zaɓen abokan haɗin gwiwarta. Nuna goyon baya ga bunƙasuwar Afirka, alhaki ne da ƙasa da ƙasa suka ɗauka tare. Rahotanni sun bayyana cewa, kwamandan rundunar sojojin Amurka dake nahiyar Afirka Stephen Townsend ya bayyana a jiya cewa, yanayin tsaro a nahiyar Afirka yana da sarƙaƙiya, Sin da Rasha sun fi yin amfani da hanyoyin diplomasiyya, da tattalin arziki,…
Read More
Ta hanyar haɗa kai ne ‘yan siyasa mata za su samu ‘yancinsu – Fatima Kadashi

Ta hanyar haɗa kai ne ‘yan siyasa mata za su samu ‘yancinsu – Fatima Kadashi

"Mijina ne ya ba ni tallafi a takarar da na fito" "Faɗuwa a siyasa ma nasara ce" Daga AISHA ASAS Sanannen abu ne mata a wannan zamani sun yunƙuro kan sha'anin siyasa, sun kuma nuna za su iya idan aka ba su dama ta ɓangaren riƙe madafun iko a ƙasar nan. Sai dai hakan ya zama wata barazana ga wasu mazan 'yan siyasa ganin cewa idan suka yi wasa hula za ta bi bayan ɗankwali ne a harkar siyasar Nijeriya.Wannan tunanin na su ne ya sa suke amfani da ƙarfin ikonsu wurin ganin sun hana mata katavus a fagen siyasa,…
Read More
Ba za mu yi watsi da burinmu na cimma nasara ba

Ba za mu yi watsi da burinmu na cimma nasara ba

Daga BILKISU XIN Ita ce Shui Qingxia, mai horar da 'yan wasan ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar Sin, tun bayan kama kujerar take ɗaukar nauyi da ƙalubale na jagorantar ƙungiyar fita daga mawuyacin hali. Tana ƙoƙari tare da ƙungiyarta don mika wata takardar amsa ta cimma gasar ta kofin Asiya ga al’ummar ƙasar baki ɗaya. Da taushin hali da jajircewarta, ta canza makomar ƙungiyarta, da makomar gungun ’yan mata, har ma da nata makoma. A shekarar 1983, Shui Qingxia mai shekarun haihuwa 17 a duniya ta samu horo kan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Makarantar Wasannin Matasa ta yankin…
Read More
Arewacin Nijeriya: Tauyayyun zakuna!

Arewacin Nijeriya: Tauyayyun zakuna!

Daga MUHAMMAD NASEER LERE Ba ƙaramin lamari ba ne ballantana a ce zai iya shiga rubibi har a manta. Na tabbata komai nisan lokaci ƙwaƙwalenmu ba za su iya mantawa da irin kisan gillar da ake mana a AREWA ba! Sannan ba za mu iya hana bakunanmu faɗin, An kasa ceto rayukanmu ba. Ina tunanin muna faɗin hakan ne domin kunnuwanmu sun ji lokacin da gwamnatinmu ke rantsuwar tsare rayukanmu. Kenan, ba za mu iya daina faɗin, an kasa ceto rayukanmu ba, har sai ranar da muka manta da kalaman gwamnati na alƙwarin tsare dukiya da rayukanmu. Ko dai mu…
Read More
Tsaftace yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta

Tsaftace yadda matasa ke amfani da zaurukan sada zumunta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A ƙarshen makon da ya gabata na samu halartar wani babban taron bita na yini biyu da ƙungiyar matasan Arewa masu amfani da zaurukan sada zumunta don isar da saƙonni, yaɗa labarai da tallata kayayyakin su na kasuwanci ta gudanar. Ƙungiyar da aka fi sani da suna Arewa Media Writers, ta shirya gagarumin bikin cika shekaru biyu da kafuwar ƙungiyar ne a garin Bauchi, wanda ya gudana a babban Hotel ɗin nan na Zaranda. Matasa daga dukkan sassan jihohin Arewa sun samu halartar wannan taro, wanda aka yi wa taken 'Rawar Da Kafofin Sada Zumunta Ke…
Read More