Editor

9513 Posts
Abu Zubaydah da aka yi wa laƙabin “daɗaɗɗen fursuna”

Abu Zubaydah da aka yi wa laƙabin “daɗaɗɗen fursuna”

Daga MINA Abokai, yau “duniya a zanen MINA” na zana wani mutum mai suna Abu Zubaydah, da aka yi wa lakabi “dadadden fursuna” dake tsare a gidan yarin Guantanamo. Hukumar leƙen asiri ta Amurka ta mai da Abu Zubaydah a matsayin “mutum mafi daraja dangane da batun ta’addanci”, amma ana tsare da shi ba tare da kai masa ƙara ko yanke masa hukunci ba, inda ake azabtar da shi har tsawon shekaru 20, duk da cewa an taba gabatar da shaidu cewa, shi ba mambar ƙungiyar Al-Qaeda ba ne. Bisa ƙididdigar da asusun Open Society Foundations na Amurka ya bayar,…
Read More
An miƙa lambar yabon zaman lafiya ta MƊD ga sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura wa Kongo(Kinshasa) karo na 25

An miƙa lambar yabon zaman lafiya ta MƊD ga sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura wa Kongo(Kinshasa) karo na 25

Daga CMG HAUSA An mika lambar yabon kiyaye zaman lafiya ta MƊD ga dukkanin sojojin kiyaye zaman lafiya su 218, da ƙasar Sin ta tura wa ƙasar Kongo (Kinshasa) karo na 25, a sansaninsu dake jihar South Kivu ta kasar a jiya Litinin. Bisa umurnin tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Kongo ta MƊD ko MONUSCO a taƙaice, an shirya bikin mika lambar yabon ga sojojin kiyaye zaman lafiya da ƙasar Sin ta tura wa ƙasar a karo na 25 jiya, inda kwamandan rundunar sojojin Deng Liang ya bayyana cewa, dukkanin sojojin ƙasar Sin sun darajanta yabon da ake…
Read More
Tagwayen titunan mota na ƙasar Sin sun haɗe kaso 95 bisa ɗari na alummun ƙasar

Tagwayen titunan mota na ƙasar Sin sun haɗe kaso 95 bisa ɗari na alummun ƙasar

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin ta kafa ƙaƙƙarfan ginshiki a fannin gina manyan titunan mota, domin haɗe sassa daban daban na yankunan ƙasar, da sauƙaƙa zirga zirgar ababen hawa, kuma tuni waɗannan manyan tituna suka haɗe kimanin kaso 95 bisa dira na yankunan ƙasar. Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai a jiya Litinin, jamii a ma'aikatar sufuri ta ƙasar Wang Tai, ya ce a yanzu haka, manyan hanyoyin ƙasar sun haɗe kaso 98.8 bisa dari na birane masu yanwan alummar da suka zarta 200,000, da manyan yankunan gudanarwa, yayin da irin waɗannan manyan tituna…
Read More
Gwagwarmayar Hajiya Gambo Sawaba

Gwagwarmayar Hajiya Gambo Sawaba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haifi Hajiya Gambo Sawaba a ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu na shekarar 1933, a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Sunan mahaifinta Isa Amartey Amarteifio (Christened Theophilus Wilcox,) ɗan asalin ƙasar Ghana ne. Ya kammala karatunsa a makarantar Ghana School of Survey. Ya yo hijira zuwa Nijeriya ne a shekarar 1910, ya zo ne don neman aiki a Nigerian Railway Corporation, daga nan kuma sai ya yanke shawarar yin zama na dindindin. Aiki ya kawo shi garin Zariya, inda a nan Christened Theophilus ya karɓi addinin Musulunci, ya sauya suna zuwa Isa. A nan…
Read More
Ya auri jikarsa kuma ya ƙi rabuwa da ita

Ya auri jikarsa kuma ya ƙi rabuwa da ita

Wani magidanci mai suna Alhaji Musa Tsafe mai shekaru 47, ya dage kan ƙin sakin jikarsa wadda ya aura shekaru 20 da suka gabata. Mutumin wanda ke zaune a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara tare da iyalinsa, ya ce, ba zai sawwaƙe wa jikar tasa ba duk da an ankarar da shi a kan haramcin igiyar auren da aka ƙulla a tsakaninsa da ita. Bayanai sun ce, matar mai suna Wasila Isah Tsafe mai kimanin shekaru 35, wadda jika ce ga babban yayan Alhaji Musa, ta haifa masa ’ya’ya takwas a tsawon shekaru 20 na aurensu. Sai dai wannan…
Read More
Likitoci sun gano kuɗaɗe da ƙusoshi a cikin wani mutum

Likitoci sun gano kuɗaɗe da ƙusoshi a cikin wani mutum

Likitoci sun shiga mamaki bayan sun gano ɗaruruwan tsabar kuɗi da ƙusoshi da batura da guntattakin gilasai bayan da wani mutum mai suna Burhan Demir daga garin Ipekyolu na ƙasar Turkiyya ya kai ƙaninsa asibiti saboda kukan ciwon ciki. A lokacin da likitocin suka yi gwajin hoton cikin mutumin ta amfani da 'Endoscopic' tare da ɗaukar hoton cikin da na’urar d-ray sun yi mamaki bayan gano abubuwa 233 a cikin mara lafiyar mai shekara 35. Abubuwan sun haɗa da tsabar ƙarafan kuɗin ƙasar Lira guda ɗaya da batura da mayen ƙarfe da ƙusoshi da gilasai da duwatsu. Daga baya likitocin…
Read More
Barazanar hari: Gwamnati ta rufe Kwalejin Kwali a Abuja

Barazanar hari: Gwamnati ta rufe Kwalejin Kwali a Abuja

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan barazanar mahara a yankin babban birnin tarayya, Abuja, ya sa Gwamnatin Tarayya ɗaukar matakin rufe Kwalejin Tarayya (FGC) da ke Kwali a ranar Litinin don kauce wa jefa rayuwar ɗalibai da malamai cikin haɗari. Gwamnati ta bada sanarwar rufe makarantar ne bayan da ta samu rahoton jami'an tsaro sun daƙile wani shirin kai harin da aka yi zargin 'yan bindiga sun yi a yankin Bwari. Wannan na zuwa ne kwanaki 21 bayan mummunan harin da 'yan bindigar da ake kyautata zaton ISWAP ne suka kai gidan yarin Kuje a Abuja. Lamarin da ya yi sanadiyar…
Read More
‘Yan Nijeriya na ci gaba da alhinin mutuwar jaruma Ada Ameh

‘Yan Nijeriya na ci gaba da alhinin mutuwar jaruma Ada Ameh

Daga AISHA ASAS Biyo bayan labarin mutuwar shaharariyyar 'yar wasan Kudu, Ada Ameh, wadda ta ke cikin ganiyar ta a masana'antar finafinai ta Nollywood, 'yan Nijeriya sun shiga alhini da kuma mamakin mutuwar jarumar wadda ta zo masu a ba-zata. Jarumar wadda ta kasance ɗaya daga cikin jaruman da ke haska shirin nan mai dogon zango na 'The Johnson', ta mutu ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022, a asibitin da ke Jihar Delta inda aka kai ta, bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani taro da ta halarta. Jarumar dai ta mutu tana da shekaru 48…
Read More
Zaratan mawaƙa mata biyar na duniya da kuma arzikinsu

Zaratan mawaƙa mata biyar na duniya da kuma arzikinsu

Daga AISHA ASAS A wannan zamani baiwar waƙa ta wadatu ga mata fiye da inda aka fito, hakan ya sanya suka fara samun wurin zama na musamman a duniyar nishaɗantarwa, kasancewar su a gaba wurin samar da nishaɗi ta vangaren waƙa. Duniya ta san da zamansu hakan ya sa suka samu ɗaya daga cikin romon da shuhura ke bayarwa, wato dukiya. Bincike ya nuna, yawaitar mata mawaƙa musamman a ɓangaren da ake kira 'rapper' ya taimaka ƙwarai wurin rage ƙalubalen da mata ke fuskanta a duniyar nishaɗantarwa. Domin sun yi ƙarfi kuma an fahimci harkar ba ta tafiya dole sai…
Read More
Alamomin rushewar zamantakewa

Alamomin rushewar zamantakewa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a filin zamantakewa na wannan makon. Sannunku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da alamommin da suke nuna cewa aurenku yana da masassarar mutuwa, wato kwanansa yana gab da ƙarewa. Kamar yadda Hausawa kan ce aure rai ne da shi, duk ranar da wa'adin ajalinsa ya zo, labudda ba ya ƙara kwana, wannan batu haka yake. Idan ajalin aure ya zo, za ka ga alamomi suna ta nunawa. An san dole da ma a zaman aure zama ne na zo mu zauna, zo mu…
Read More