Editor

9513 Posts
Xi ya aike da saƙon taya murna ga taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na Sin da Afirka karo na biyu

Xi ya aike da saƙon taya murna ga taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na Sin da Afirka karo na biyu

Daga CMG HAUSA Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murna ga taron dandalin tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro na ƙasar Sin karo na biyu. Xi ya jaddada cewa, ƙasashen Sin da Afirka abokai ne na kwarai, kuma abokan hulɗa, kana 'yan uwa na ƙwarai, waɗanda ke tsayawa tsayin daka a kowane irin hali suna kuma taimakon juna. A halin yanzu, duniya tana fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba gani ba a cikin ƙarni cikin sauri. Kuma har yanzu annobar COVID-19 tana yaɗuwa, kuma ƙalubalen tsaro daban-daban na ci gaba da bayyana, inda…
Read More
An ƙaddamar da gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to meet you”

An ƙaddamar da gasar bidiyo ta matasan Sin da Afrika ta “Great to meet you”

Daga CMG HAUSA A yau Litinin aka ƙaddamar da gasar tsara bidiyo ta matasan Sin da Afrika mai taken “Great to Meet You” ta babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG, wanda ke zaman wani yunƙuri na ganin kyan bangarorin biyu da kuma ƙulla abota. Manufar wannan gasa ita ce, amfani da gajeren bidiyon da aka tsara wajen samar da dandalin musaya da koyo daga juna tsakanin matasan Sin da Afrika, da bayyana salon matasan Sin da Afrika tare da inganta ɗorewar abota tsakanin Sin da Afrika. Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa
Read More
Ƙungiyar ’yan kasuwa ta Abuja za ta zuba jari a Amurka

Ƙungiyar ’yan kasuwa ta Abuja za ta zuba jari a Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar ’yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI), ta buƙaci ’yan kasuwar Nijeriya da su yi amfani da jerin bayanan zuba jari da za su yi don mallakar kasuwanci a Amurka. Shugabar ƙungiyar na ACCI, Victoria Akai, ta yi wannan bayani a ranar Laraba a wani taron manema labarai a Abuja, don bayyana jerin bayanai kan damar zuba jari a Amurka, mai taken; ‘EB-5 Fasfo Series’. Taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Oktoba a cibiyar hada-hadar kasuwanci ta ACCI da ke Abuja, kamfanin 'Invest In the USA', IIUSA, tare da haɗin gwiwar…
Read More
KKDA ta bai wa mata 95 jari a Gombe

KKDA ta bai wa mata 95 jari a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar ci gaban unguwar Kumbiya-kumbiya Development Association (KKDA), ta gina azuzuwan karatu da kuma manyan kwalbatoci uku a unguwar, sannan ta sama wa wasu mata 95 jarin naira dubu 10 don bunƙasa sana'oinsu. Shugaban ƙungiyar, Dakta Ahmed Yarmama shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce, a Gombe ƙungiyar ta zama abin misali da wasu unguwanni suke zuwa kwaikwayon irin ayyukan da suke yi. Ya ƙara da cewa, sun tara kuɗin ƙungiyar ne a banki, inda daga baya ya ga ci gaba da ajiye su bai da amfani gara su gyara unguwarsu kuma su…
Read More
Gidauniya Hausari za ta sa ’ya’ya mata 150 makaranta kyauta a Yobe

Gidauniya Hausari za ta sa ’ya’ya mata 150 makaranta kyauta a Yobe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata gidauniya mai rajin haɓaka harkar ilimin ’ya’ya mata a jihar Yobe, 'Hausari Female Education Support Foundation', za ta saka yara mata 150 makarantun boko kyauta a jihar. Shugabar gidauniyar, Hajiya Hafsatu Alhaji Ado, ta ce, za su ba da tallafin ne a ƙoƙarinsu na mara wa aniyar gwamnatin jihar baya wajen inganta ilimim ’ya’ya mata. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke zantawa da manema labarai a Gombe ranar Lahadi, inda ta ce, ciyar da ilimin ’ya’ya mata gaba ne maƙasudin kafa gidauniyar tasu. Hajiya Hafsatu ta ce, gidauniyar sabuwa ce da aka…
Read More
An haɗa na’urar Wentian da na’urar Tianhe a sararin samaniya

An haɗa na’urar Wentian da na’urar Tianhe a sararin samaniya

Daga CMG HAUSA Rahotanni daga ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin (CMSA) sun ce, bayan da aka yi nasarar harba na’urar Wentian, wani muhimmin ɓangare na farko na tashar binciken sararin samaniya, har ta shiga falaki cikin nasara, da misalin ƙarfe 3 da minti 13 na safiyar yau Litinin 25 ga wata ne, na’urar Wentian ta yi nasarar haɗewa da bangaren gaba na na’urar Tianhe a sararin samaniya, al’amarin da ya shafe tsawon awa 13. Wannan shi ne karon farko da wasu manyan na’urorin binciken sararin samaniyar ƙasar Sin guda biyu, masu nauyin ton 20, wato…
Read More
Tsadar fulawa: Ƙungiyar masu gidajen burodi ta tsunduma yajin aiki

Tsadar fulawa: Ƙungiyar masu gidajen burodi ta tsunduma yajin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Masu Gidajen Burodi ta Nijeriya (PBAN) ta ce, ta kammala dukkan shirye-shiryen fara yajin aikin kwana huɗu daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, a duk faɗin ƙasar. Masu sana’ar dai za su tsunduma yajin aikin ne don nuna damuwarsu kan yadda tsadar fulawa da sauran kayan haɗi ke ƙara tagayyara sana’arsu. Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Emmanuel Onuorah da kuma mai magana da yawunta, Babalola Thomas, sun kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da cajinsu kaso 15 cikin 100 na fulawar da ake shigowa da ita Nijeriya. Sun kuma nemi Hukumar da ke…
Read More
Mansur Gulma da magoyabayansa sun fice daga APC zuwa PDP

Mansur Gulma da magoyabayansa sun fice daga APC zuwa PDP

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Alhaji Mansur Adamu Gulma tsohon ɗan takarar ɗan majalisar dokoki a Jam'iyyar APC daga  ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ya bar Jam'iyyar APC zuwa PDP tare da magoyabayan sa. Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi, Sanata mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa shi ne ya karɓe su jiya Alhamis a garin Gulma ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mansur Adamu Yargayra. Alhaji Mansur Adamu Yargayra ya bayyana cewa dalilan da suka sanya su barin Jam'iyyar APC zuwa PDP sun haɗa da rashin adalcin da ake yi da kuma kama karya a Jam'iyyar APC a jihar Kebbi bakiɗaya.…
Read More
Yadda jam’iyyar APC ke tangal-tangal a Kebbi

Yadda jam’iyyar APC ke tangal-tangal a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Tun bayan  tirka-tirkar zaɓen fid da gwanin yantakarar kujerar gwamna a jihar Kebbi Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta ɗauki hanyar rugujewa sanadiyyar rashin gaskiyar da mafi yawan 'ya'yan jam'iyyar ke ganin an tafka da kuma irin yadda salon mulkin da ake yi da ya saɓa wa hankali. Jihar Kebbi dai tana daga cikin jihohin da suka taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ganin jam'iyyar APC ta kafa gwamnati  a dukkan matakai. Tun kama daga ƙananan hukumomi zuwa jiha, har tarayya a shekarar 2015, lokacin da iskar guguwar Buhari ta kaɗa. Duk da…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Kano ta bajekolin mutane 198 masu laifi daban-daban

Rundunar ‘yan sandan Kano ta bajekolin mutane 198 masu laifi daban-daban

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da masu laifuffuka daban-daban a faɗin jihar cikin watanni uku don samar da zaman lafiya da kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Tabbatar da hakan na zuwa ne sa'ilin da rundunar take gabatar wa da manema labarai masu laifuffukan a hedikwatarta da ke Bampai a ranar Alhamis da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Maigirma Kwamishinan 'Yan Sanda da ake wa laƙabi da 'Nagari Na Kowa', CP Sama'ila Shu'aibu Dikko. A jawabinsa lokacin da yake gabatar da masu laifuffukan, kwamishinan ya yaba wa jami'an rundunar da…
Read More