Editor

9513 Posts
Zanga-zangar lumana za a yi ba ta tashin hankali ba – Martanin ‘yan ƙwadago ga DSS

Zanga-zangar lumana za a yi ba ta tashin hankali ba – Martanin ‘yan ƙwadago ga DSS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeirya ta ce babu gudu babu ja da baya kan zanga-zanagar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar. ’Yan ƙwadagon na martani ne ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) bisa gargaɗin da ta yi cewa ƙungiyar ta dakatar da ƙudirin da ta gabatar na zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu. A baya dai hukumar ta shawarci ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya NLC da takwararta ta TUC da su janye matakin da suka ɗauka, inda ta ce hakan zai tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Sai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An tsige Shugaban Majalisar Zamfara

Da Ɗumi-ɗumi: An tsige Shugaban Majalisar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau An tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon Bilyaminu Moriki, yayin da Hon. Bashar Gummi ya karɓi ragamar shugabancin majalisar. Wakilin mu ya tattaro cewa, mambobi 18 cikin 24 sun amince da tsige shugaban majalisar a wani taron gaggawa da suka yi a daren Alhamis. MANHAJA ta gano cewa tsigewar ba ta rasa nasaba da ƙudirin da ɗaya daga cikin mamba mai wakiltar mazaɓar ƙaramar hukumar Maru, Hon. Nasiru Abdullahi ya kawo gaban majilisar yayin taron gaggawar da suka gudanar a jiya na buƙatar a cire shi. Mambobi masu daraja za su iya zaɓar wanda…
Read More
Afrika ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Gaza

Afrika ta yi tir da hare-haren Isra’ila a Gaza

*Falasɗinu ta yi maraba da taron AU Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin ƙasashen Africa sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke ƙaddamarwa kan yankin Gaza da sunan kare kai, yayin da suka buƙaci ƙasar ta dakatar da varin wutar  ba tare da vata lokaci ba. Moussa Faki Mahamat, shugaban majalisar gudanarwar ƙungiyar ta AU ya ce wannan luguden wuta, babu abinda ke cikinsa illa cin zali da cin zarafi, kuma lokaci ya yi da duniya za ta mayar da Isra’ila cikin hayyacin ta. Kalaman na Faki na zuwa ne bayan doguwar maƙala da Prime ministan Falasɗinu…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ba da belin tsohon Gwamnan Kwara kan N50m

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ba da belin tsohon Gwamnan Kwara kan N50m

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Ilorin, Jihar Kwara kuma ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Evelyn Anyadike, ta ba da belin tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Alh AbdulFatah Ahmed. Kotu ta ba da belin ne bisa sharuɗɗa da suka haɗa da biyan Naira miliyan 50 ga kotu da shaida wanda ya mallaki fili aIlorin da sauransu. Ana da ran tsohon gwamnan ya ci gaba da zama a hannun EFCC har zuwa lokacin da zai cika sharuɗɗan.
Read More
’Yan sanda sun musanta sace matafiya 26 a hanyar Gusau zuwa Sakkwato

’Yan sanda sun musanta sace matafiya 26 a hanyar Gusau zuwa Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara ta musanta ikirarin sace fasinjoji 26 da aka yi a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato. Rahotanni sun bayyana cewa, wasu gungun 'yan bindiga sun tare hanya tare da garkuwa da masu ababen hawa. Sai dai ’yan sandan sun yi gaggawar mayar da martani tare da fatattakar ’yan bindigar, lamarin da ya maido da zaman lafiya a yankin. Kakakin 'yan sandan Yazid Abubakar ya bayyana cewa yayin da ‘yan bindigar suka tare hanyar, babu wani fasinja da aka sace. Ya kuma jaddada cewa ’yan sanda sun yi nasarar tarwatsa ’yan bindigar, tare…
Read More
Tinubu da Atiku sun yi musayar yawu kan taɓarɓarewar tattalin arziki

Tinubu da Atiku sun yi musayar yawu kan taɓarɓarewar tattalin arziki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fadar shugaban ƙasa da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar sun yi ta cacar baki mai zafi game da manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, musamman faɗuwar darajar Naira. Tsohon mataimakin shugaban Nijeriyan ya yi doguwar magana a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya zargi Bola Tinubu da jefa tattali a matsala. Atiku Abubakar yana ganin kura-kuren gwamnatin Tinubu sun gurgunta tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan ya jawo tashin da Dala ta ke yi. A jawabinsa, Atiku wanda ya zo na biyu a zaɓen 2023 ya ce, kyau a canja irin salon da ake…
Read More
Abubuwan da ya kamata a sani kan ƙudirin ƙirƙirar ’yan sandan jihohi

Abubuwan da ya kamata a sani kan ƙudirin ƙirƙirar ’yan sandan jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙudirin da ke neman a yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima domin bai wa gwamnoni damar naɗa kwamishinonin ’yan sandan jihohi a Nijeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi ƙasar. Ƙudirin wanda 'yan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen 'yan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a faɗin ƙasar. Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar…
Read More
Laifin fyaɗe: Kotu ta yanke wa Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi

Laifin fyaɗe: Kotu ta yanke wa Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Alhamis ne wata kotu a ƙasar Sifaniya ta yanke wa tsohon ɗan wasan Brazil Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi bayan samunsa da laifin yi wa wata budurwa fyaɗe a wani gidan rawa na Barcelona a watan Disamban 2022. Wata sanarwa da kotun Barcelona ta fitar ta ce "Wadda abin ya shafa ba ta yarda ba." Masu gabatar da ƙara sun buƙaci da a yanke wa ɗan wasan da ya lashe gasar zakarun Turai hukuncin ɗaurin shekaru tara a gidan yari, sai kuma na shekaru 10 na gwaji. Ɗaya daga cikin 'yan…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi awon gaba da 20 a Neja

‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi awon gaba da 20 a Neja

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Neja sun kai hari a yankin Basa da ke hayin Ƙaramar Hukumar Shiroro a jihar da safiyar Alhamis, inda suka kashe mutum biyu. Majiyarmu ta ce sun kuma tagayyara mutum guda sannan sun yi awon gaba da aƙalla mutum 20. Wani mazaunin yankin ya shaida wa majiyarmu cewa, kusan makonni biyu ke nan da 'yan bindingar ke cin karensu ba babbaka a yankin inda suke kashe mutane, su kwashi dabbobi tare ƙona dukiyoyin jama'a. Majiyar ta ƙara da cewa, a halin da ake ciki wanda aka raunata sakamakon harin yana asibiti yana karɓar…
Read More
Kakakin Majalisar Jihar Zamfara na fuskantar barazanar tsigewa

Kakakin Majalisar Jihar Zamfara na fuskantar barazanar tsigewa

Daga BASHIR ISAH Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Moriki, na fuskantar barazanar tsigewa daga mafiya rinjayen mambobin majalisar. Ya zuwa haɗa wannan rahoto, MANHAJA ta tattaro cewar galibin 'yan majalisar na gudanar da taro a harabar majalisar da yammacin ranar Alhamis kan yadda za su tsige kakakin majalisar. Kazalika, ziyarar da wakilinmu ya kai harabar majalisar ya gano yadda aka rufe harabar majalisar da kuma girke jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan danda da sibul difens a cikinta. Bincike ya nuna hatta sandan majalisar bai tsira ba, don kuwa an samu wasu da suka yi awon gaba…
Read More