ukarofi

11000 Posts
Tinubu ya gana da Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka

Tinubu ya gana da Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Amurka

Shugaba Tinubu yayi kira da a samu alaƙa mai karfi tsakanin hukumomin yaƙi da ta'addanci na Najeriya da kuma hukumar leƙen asiri da ke ƙasar Amurka. Shugaban yayi wannan kira ne a yayin ganawarsa da daraktan hukumar leƙen asirin Chritopher Asher a fadar shugan ƙasan da ke Abuja. Manyan jami'an tsaro da suka halarci taron sun haɗa da, Malam Nuhu Ribado, Babban sufeton yan sanda, Kayode Efbetekun, shugaban hukumar yan sanda farin kaya, Yusuf Bichi, shugaban hukumar da ke yaƙi da fatucin miyagun ƙwayoyi, Birgediya Janar Buba Marwa, da sauransu. Shugaban yayi murna ƙwarai dagaske da ziyarar. Wanda yace hakan…
Read More
An bankaɗo badaƙalar ɗaukar aiki a wasu ma’aikatun gwamnatin Kano

An bankaɗo badaƙalar ɗaukar aiki a wasu ma’aikatun gwamnatin Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci ta ƙasa da Rashawa reshen Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarorin dindindin guda uku domin amsa tambayoyi kan badaƙalar sayar da fom ɗin aiki a Ofishin Shugaban Ma’aikata. Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa a Kano ranar Laraba cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a badaƙalar. Ya ce, tuni dubban masu neman aiki damfarar ta shafa.“Bincike na farko ya gano…
Read More
Wasu sanannu ke ba yan ta’adda kariya- Gwamnan Zamfara

Wasu sanannu ke ba yan ta’adda kariya- Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara ya zargi wasu sanannun yan Najeriya da taimakawa wajen sakin wasu yan ta'adda waɗanda suka amsa laifukansu na kisan kai. Gwamnan ya nuna rashin jin daɗi bayan da ya samu labarin wasu masu ƙarfi a gwamnati sun taimaka wajen bada belin yan ta'addan. Gwamnan na wannan bayanin ne a ma'aikatar sharia ta Jihar Zamfara, inda yake cewa wasu yan ta'adda da gwamnatin shi ta kama, ya samu labarin kotun da ke Abuja ta bada belin su. Yan ta'addan su amsa laifukan su na kisan kai, da kuma makamai da aka kama su dashi. Amma hakan bai hana…
Read More
Yadda sojoji suka halaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Yadda sojoji suka halaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Daga MADHI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya sun bayyana cewa, sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.Cikin wata sanarwa kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da KatsinaYa ƙara da cewa, Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da…
Read More
Dangote ya fallasa masu yunƙurin dakatar da matatarsa

Dangote ya fallasa masu yunƙurin dakatar da matatarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mamallakin rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka na cikin gida da waje, waɗanda ya bayyana a matsayin “mafiya”, suna yunƙurin yin zagon ƙasa a aikin matatar man da ya kai Dala Biliyan 19 a Legas.A yayin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na Afreximbank, Aliko Dangote ya ce, ƙungiyar mafia masu safarar mai sun fi ƙarfin masu safara miyagun ƙwayoyi, waɗanda su ne ke neman riƙe masa masana'anta.“To, na san cewa akwai fitina. Amma ban san cewa mafiyan man fetur sun fi ƙarfin mafiyan ƙwayoyi ba. Na tabbatar da…
Read More
Ƙananan hukumomi: Kotun ƙoli ta sa ranar sauraron ƙarar Gwamnatin Tarayya

Ƙananan hukumomi: Kotun ƙoli ta sa ranar sauraron ƙarar Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ƙoli ta ajiye hukunci a gaban gwamnatin tarayya kan gwamnonin jihohi 36 da ke neman cikakken cin gashin kansu ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.Mai shari’a Garba Lawal a ranar Alhamis ya bayyana cewa za a sanar da ɓangarorin da ke cikin lamarin da zarar an yanke hukunci. Ya sanar da jingine hukuncin ne bayan da kwamitin mutum bakwai na Kotun ƙoli ya amince da matakin da babban lauyan gwamnatin tarayya AGF, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar a madadin gwamnatin tarayya, da na gwamnonin jihohi 36.A zaman da aka yi ranar…
Read More
Kotu ta sallami manyan masu ruwa da tsaki na Binance

Kotu ta sallami manyan masu ruwa da tsaki na Binance

Daga Karofi Usman Babban kotun Ƙasa da ke zamanta a Abuja ta sallami Tigran Gambaryan, dan shekara 39 ɗan asalin ƙasar Amurka da kuma Nadeem Anjarwalla waɗanda ake zargi da rashin biyan haraji. Dukkansu masu ruwa da tsaki a kafar da ake hada hadar kirifto wato Binance wanda gwamnatin Najeriya ke ƙara ta hannun hukumar FIRS a kan rashin biyan haraji. Duk da cewa Binance ba tada wakili na doka a Najeriya, bai hana an karanta tuhume tuhemen ga Gambaryan ba.Mai wakiltar shi yace wanda yake wakilata ba a bashi tuhumar ba hannu da hannu, don haka bai kamata a…
Read More
Rikicin masarauta: Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano Naira miliyan 10

Rikicin masarauta: Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano Naira miliyan 10

A yau ne babbar Kotun Ƙasa da ke jihar Kano ta ci tarar gwamnatin Kano Naira Miliyan 10 sabida take haƙƙin dan adam da tayi wa sarkin da aka tuɓe Aminu Ado Bayero Wannan na zuwa ne bayan da Alƙalin kotun Mai Shari’a Muhammad Liman ya bayyana cewa kotun na da hurumin sauraron ƙarar Aminu Ado ɗin. Yayin da mai Sharia Simon Amobeda yake karanto hukunci a yau, Ya ƙara da cewa Aminu Ado na da yancin yin yawo cikin garin kano a ko da yaushe. Sai dai kotun ba ta bada umarnin fitar da Sarki Sanusi daga gidan rumfa…
Read More
A Jihar Neja:’Yan bindiga sun mamaye gonakin mutum 3,000

A Jihar Neja:’Yan bindiga sun mamaye gonakin mutum 3,000

Sama da mutane 3,000 da suka rasa matsugunansu a garin Erena bayan sun tsere daga yankunansu a kwanakin baya sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, inda a halin yanzu suke fuskantar annobar yunwa sakamakon ƙarancin abinci.An gano cewa, ’yan gudun hijirar na fama da yunwa a Erena duk da cewa, suna da wadataccen abinci a gonakinsu da ke yankinsu, yankin da ’yan bindiga suka mamaye kuma suka tare su isa ga gonakin.Blueprint Manhaja ta gano cewa, mutane uku da suka yi ƙoƙarin samun abinci ga iyalai masu fama da yunwa daga ƙauyensu na…
Read More