ukarofi

11000 Posts
Rikicin Masarautar Kano ya caɓe bayan umarnin kotu da na ’yan sanda

Rikicin Masarautar Kano ya caɓe bayan umarnin kotu da na ’yan sanda

Daga NASIR S. GWANGWAZO Daga dukkan yanayin babu alamun lalubo warware rikicin da ke addabar Masarautar Kano a nan kusa bisa la’akari yadda har yanzu kotu da jami’an tsaro ke cigaba da taka rawa a cikin lamarin.A jiya Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Alƙali Muhammad Liman ta yanke hukuncin cewa, ta na da hurumin sauraron ƙarar da aka kai gabanta kan tuɓaɓɓen Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, tsigaggen Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babban ɗan Agundi, ke ƙalubalantar sauke su.Jim kaɗan bayan hakan kuma, sai Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar…
Read More
Har aikin noma na yi don koyon aiki a Kannywood – Maskwani

Har aikin noma na yi don koyon aiki a Kannywood – Maskwani

Daga IBRAHIM HAMISU Muhammad Abdullahi Uzairu, wanda aka fi sani da Sanin Inna Maskwani, ķwararren mai kula da sautin fim (Saund Engineer) ne a Masana'antar Kannywood. A tattaunawarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU, a Kano, za ku ji yadda yake gudanar da aikinsa a cikin shekaru 13 da ya yi a masana'antar fim. Ku biyo mu: MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatun mu.MASKWANI: Sunana Muhammad Abdullahi Uzairu wanda akafi sani da Sanin Inna maskwani. MANHAJA Ko za ka bamu taƙaitaccen tarihinka?MASKWANI Ni ɗan Kano ne anan aka haife ni anan nake rayuwata, sannan…
Read More
Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Manhaja, da fatan ba ku ƙosa da wannan darasi na atisaye ba. A yau da yardar mai dukka za mu taɓo wani ɓangare da kusan zan iya cewa ya fi adabbar mutane, amma rashin sani kan sa ayi masa wata fassarar da ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa. Da yawa daga cikin wasu matsaloli da suka dangance ciwo da muke cewa matsala ce ta mutanen ɓoye, ko sammu da jifa, zuwa duk wata damuwa da ta shafi rikeɗewar tunani, takan samu ne ta sanadiyyar damuwa.…
Read More
Yawancin auren dole da ake yi wa yara ana gina shi ne bisa son zuciya da kwaɗayi – Lantana Jafar

Yawancin auren dole da ake yi wa yara ana gina shi ne bisa son zuciya da kwaɗayi – Lantana Jafar

Daga AISHA ASAS A wannan satin shafin Gimbiya ya karɓi baƙuncin mata guda biyu, waɗanda suka kasance fitattu kan sha’anin bayar da gudunmuwa a ɓangaren tarbiyya da kuma zamantakewar aure.Dalilin gayyatar tasu dai ba ɓoyayye ba ne, kasancewar shafin namu na duba ne kawai ga bukatun uwayen gida, hanyoyin da za su bi kan gyara zamantakewar su ta aure ko zaman gida, zuwa ga tarbiyyar 'ya'yansu da kuma zaburarwa kan neman na kai.Baƙin namu za su amsa mana tambayoyi ne kan ɗaya daga cikin matsalolin da ke ciwa ƙasar Hausa ko in ce mata tuwo a ƙwarya, wato matsalar auren…
Read More
Yawan karatun littattafan marubutan Nijeriya ne ya sanya na goge a rubutun Hausa – Ikilima Adam

Yawan karatun littattafan marubutan Nijeriya ne ya sanya na goge a rubutun Hausa – Ikilima Adam

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ikilima Adam ɗaya ce daga cikin marubutan adabin Hausa da ake da su a maƙwaftan Nijeriya. Duk da kasancewarta 'yar ƙasar Jamhuriyar Benin, wacce ta ke rayuwa a cikin harshen Faranshi, amma da wuya mai karatu ya fahimci haka a cikin rubuce-rubucen da take yi, saboda yadda ta saje da marubutan ƙasar Hausa. Sannan ita kaɗai ce a tarihin rubutun Hausa da aka samu matashiyar mace ta shirya gasar rubutun gajeren labari da bai wa marubuta damar baje basirarsu kan matsalolin rabuwar aure. Iqilima, wacce ta kafa Gidauniyar Tallafawa Harkokin Adabi ta Kyauta Daga Allah Foundation…
Read More
Ƙaruwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta

Ƙaruwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta

A cikin watan Yunin 2013, Hukumar Kula da Ilimi, Zamantakewa da Al’adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (UNESCO), ta sanar da cewa, Nijeriya ta zama ƙasa mafi yawan al’umma a duniya da ke da yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta. Sauran ƙasashen da aka bayyana sunayensu a cikin rahoton sun hada da: Pakistan masu yara miliyan 5.1m marasa zuwa makaranta, Ethiopia 2.4, Indiya 2.3, da sauransu. A shekarar 2018, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta mayar da adadin zuwa miliyan 12.5, inda aka ɗora alhakin ƙaruwar hakan da hare-haren ta’addanci ga makarantu a Arewa. Duk da alƙawarin da shugaban ƙasa…
Read More
Tsaro: Harkar na kawo ruɗani a Nijeriya

Tsaro: Harkar na kawo ruɗani a Nijeriya

Assalamu alaikum, edita. Da fatan muna lafiya? Harkar tsaro, wani rukuni ne daga cikin manyan rukunan gudanar da gwamnatin. Wanda hakan ya sa ake ware wa harkar makudan kudi don wanzar da zaman lafiya. Ko wace ƙasa da ta ke ikirarin cewa ta cika ƙasa, dole ne sai da samar da tsaron, domin kuwa idan babu zaman lafiya to babu gwamnati. To irin hakan, wasu ƙungiyoyi da suka ɗaukar wa kansu tada zaune tsaye, sannan da hadafin cewa suna yaƙi ne don nema yancinsu, ya sa matsalar tsaro ya haɗa dangi da siyasa. Duk da cewa, babban abinda ke haifar…
Read More
MAKAMASHI: Kururuwa ba ta hana ɓarawo sata

MAKAMASHI: Kururuwa ba ta hana ɓarawo sata

Tare da Bashir Mudi Yakasai Ma’abota hikima na cewa “a-tara-a-tara ba ta hana ɓarawo sata”, saboda haka duk wata kururuwa da ’yan ƙasa za su yi, saboda ɓarayin biro da abokar hurɗarsu, wato ɓarayin zaune na gida da na ƙetare, ba za su daina ba, sai dai su fito da sababbin dabaru na duk wani tarko da aka kafa, domin wai a kama su. A taƙaicen taƙaitawa maganinsu hakunci mai tsanani, musamman hukuncin da ya ke da tozartawa, domin babu wulakanci da ɗan adam ya guda illa tozartawa domin ciwo ne da baya warkewa har abadan-abadan.Wannan wani mubuɗi ne ga…
Read More
Tinubu da Shettima sun kashe Biliyan N8.6 wajen tafiye-tafiye cikin wata uku

Tinubu da Shettima sun kashe Biliyan N8.6 wajen tafiye-tafiye cikin wata uku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, da Uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu sun kashe aƙalla Naira Biliyan 5.24 wajen balaguron gida da waje tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2024.Wani bincike da aka yi ta hanyar amfani da GovSpend, wani dandalin fasaha na jama'a da ke bin diddigin yadda Gwamnatin Tarayya ke kashe kuɗaɗe, ya nuna cewa an ware Naira biliyan 1.35 don tafiye-tafiyen shugaban ƙasa da kuma abubuwan da suka shafi hakan cikin watanni uku.Bugu da ƙari, an yi amfani da Naira Biliyan 3.53 wajen tafiya ƙasashen waje yayin balaguro 10, sannan…
Read More
Wasu Gwamnoni sun kashe biliyan N960 wajen walwala a wata uku

Wasu Gwamnoni sun kashe biliyan N960 wajen walwala a wata uku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin ƙasar nan 30 suka kashe maƙudan kuɗi wajen sayen kayan kwalam da maƙulashe yayin taruka da tafiye-tafiyensu cikin watanni uku.An gano cewa a cikin watanni uku kacal, gwamnonin sun kashe Naira Biliyan 986.64 domin walwalarsu yayin gudanar da taruka.An tattaro alƙaluman ta hanyar amfani da bayanan da shafin BudgIT ke wallafawa wanda ke ɗauke da bayanan kuɗin da gwamnatoci ke kashewa a jihohinsu.Rahotanni sun gano cewa jihohin sun kashe Naira Biliyan 5.1 wajen sayawa baƙi abin maƙulashe, inda aka ɓatar da biliyan N4.67 a matsayin alawus na zama ga jami’an…
Read More