12
Jun
Daga NASIR S. GWANGWAZO Daga dukkan alamu kotunan da ke sauraron taƙaddama kan gadon kagarar Masarautar Kano za su zauna a rana guda ne bayan da a jiya Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ta sanya ranar 13 ga Yuni, 2024, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci game da taƙaddama kan huruminta na sauraron shari’a kan masarautar. Wannan rana da Babbar Kotun Tarayya ta sanya ya zo daidai da ranar Babbar Kotun Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ne a ranar 28 ga Mayu, 2024.Idan za a…
