13
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, da Uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu sun kashe aƙalla Naira Biliyan 5.24 wajen balaguron gida da waje tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2024.Wani bincike da aka yi ta hanyar amfani da GovSpend, wani dandalin fasaha na jama'a da ke bin diddigin yadda Gwamnatin Tarayya ke kashe kuɗaɗe, ya nuna cewa an ware Naira biliyan 1.35 don tafiye-tafiyen shugaban ƙasa da kuma abubuwan da suka shafi hakan cikin watanni uku.Bugu da ƙari, an yi amfani da Naira Biliyan 3.53 wajen tafiya ƙasashen waje yayin balaguro 10, sannan…
