Kasuwanci

Tsaro: Tsarin da ake bi ba shi da tasiri – Kakakin Majalisar Wakilai

Tsaro: Tsarin da ake bi ba shi da tasiri – Kakakin Majalisar Wakilai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya bayyana a ranar Talata cewa Majalisar Tarayya za ta yi taro na musamman dangane da gagarimar matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya baki daya. Ya bayyana haka yayin da aka koma zaman majalisa, inda ya ke cewa matsalar tsaro a kasar nan ta yi muni kuma ta kazanta matukar gaske. “Ina bada shawarar gudanar da Taron Majalisar Tarayya kan Matsalar Tsaro. Taron zai kasance ya zama wurin da za a bijiro da shawarwari daga bakin masu ruwa da tsaki a bangarori da dama, kamar jami’an tsaro, sarakunan gargajiya,…
Read More
Farashin man fetur zai sauka, inji Gwamnan CBN

Farashin man fetur zai sauka, inji Gwamnan CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farashin man fetur a Nijeriya zai daidaita a bana yayin da matatun mai na gwamnati da na masu zaman kansu suka fara aiki. Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana haka. Ya yi magana ne a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, a wajen kaddamar da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Nijeriya (NESG) 2024 Rahoton Muhimmanci na Macroeconomic Outlook a Legas. Mista Cardoso ya ce, ana sa ran daidaitawa ko rage farashin man fetur yana da tasiri mai nisa a sassa daban-daban, yana ba da gudummawa sosai ga ingantaccen tattalin arziki da juriya…
Read More
Tarar Kwastom babu-gaira babu-dalili ce babban matsalarmu – Ƙungiyar ’yan kasuwar Arewa

Tarar Kwastom babu-gaira babu-dalili ce babban matsalarmu – Ƙungiyar ’yan kasuwar Arewa

Daga JOHN D. WADA, A Lafiya A kwanan nan ne  dai wata hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar arewacin kasar nan bakidaya da ake kira Northern Traders Association a turance wadda ta kunshi duka jihohin arewa na kasar nan 19 ta gudanar da wani gagarumin taron ta a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa don tattauna wasu matsaloli da kalubale dake addabar ‘ya’yan kungiyar bakidaya. A jawabinsa na maraba Shugaban kungiyar na kasa alhaji Baba Usman Jos wanda mataimakinsa Alhaji Jahi Abdullahi ya wakilce shi ya bayyana cewa, kungiyar ta ga ya dace ne ta hada babban taron don samun damar tattauna…
Read More
Gombe na gab da zarta Kano a fuskar kasuwanci – Adamu Baba

Gombe na gab da zarta Kano a fuskar kasuwanci – Adamu Baba

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Bayan dogon nazari da ya yi, fitaccen matashin dan kasuwan nan na Gombe, Alhaji Adamu Baba, sai ya yanke hukunci cewa, Jihar Gombe na gab da kamo Kano wajen kasuwanci, kuma nan da shekaru uku ko biyar masu zuwa, za ta zarta cibiyar kasuwancin ta Arewa. Dan kasuwar ya yi wannan kiyasin ce da yake hira da  wakilinmu a harabar wajen kasuwancinsa a Gombe City Stores, da ke tsakiyar birnin Gombe ranar Jumma’ar da tagabata, yana mai cewa, “ko shakka babu ganin yadda hada-hadar kasuwanci da cinakayya ke qara bunkasa a kullum a wannan Jihar…
Read More
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Arewa sun gudanar da babban taro a Nasarawa

Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Arewa sun gudanar da babban taro a Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A ’yan kwanan nan ne wata hadaddiyar Kungiyar 'Yan Kasuwar Arewacin Kasar nan bakidaya da ake kira 'Northern Traders Association' a Turance wadda ta kunshi duka jihohin arewa na kasar nan 19 ta gudanar da wani gagarumin taron ta a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa don tattauna wasu matsaloli da kalubale da ke addabar ’ya’yan kungiyar bakidaya. A jawabin sa na maraba Shugaban kungiyar na kasa alhaji Baba Usman Jos wanda mataimakin sa alhaji Jahi Abdullahi ya wakilce shi ya bayyana cewa kungiyar ta ga ya dace ne ta hada babban taron don…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanoni bakwai da su rarraba man Ɗangote

Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanoni bakwai da su rarraba man Ɗangote

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai manyan kamfanonin dillancin mai guda bakwai da muke da su a Nijeriya sun yi rajista tare da kamfanin tace man Dangote domin rarraba tataccen mai ta hanyar sara da sarar da shi. Wato dai man fetur din da matatar Dangoten wacce aka gina ta a kan Naira biliyan 20 ta samar. A ranar Lahadin da ta gabata ne dai su wadannan kamfannin dillancin a qarqashin shugabancin Kungiyar Manyan dillalan Man feturta Nijeriya (MOMAN) ita ce ta tabbatar da cewa,  bayan yin rajistar tasu, za su iya cigaba da rarraba man fetur din…
Read More
CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

CBN ya mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shiraya don mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wata takardar yarjejeniyar cikin gida wacce aka ba wa majiyarmu damar samu. Wannan yunkuri a cewar wani jami’in CBN ɗin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, an yi ne domin a rage cinkoso a babbar shalkwatar bankin da ke Abuja. Kodayake wasu daga cikin ma’aikatan na CBN ɗin sun yi tirjiya a kan komawa legas ɗin saboda suna ganin cewa wannan lamari an yi shi ne saboda qabilanci zalla ba don wani…
Read More
CBN ya rushe shugabancin bankunan Union, Keystone, Polaris da kuma Titan Trust

CBN ya rushe shugabancin bankunan Union, Keystone, Polaris da kuma Titan Trust

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya fara kaddamar mataki a kan rahoton da mai bincike na musamman na Babban Banki Nijeriya (CBN) da sauran abubuwan da suka dangance shi, Jim Obazee ta hanyar rushe shugabancin gudanarwa na Bankin Titan Trust da wasu guda uku. Majiyarmu ta bayyana ragowar bankunan da aka kaddamar wa wannan hukuncin kansu sun hada da Bankunan Union, Polaris, da kuma Keystone. The kwamitin daraktoci da shugabannin zartarwa na bankunan an gayyace su wani taron ganawa a ranar Larabar da ta gabata 10 ga watan Janairu 2024 inda mataimakin CBN a bangaren tsarin kudi…
Read More
Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Kafafen Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ta bayyana cewa akwai yiwuwar masu amfani da layin sadarwa na kamfanin Globacom su fuskanci kwarya-kwaryar dakikewa wajen kiran layukan sadarwa na kamfanin MTN. Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ran Litinin wadda ta samu sa hannun Daraktan Sashen Hulda da Jama'a, Reuben Muoka. NCC ta ce za a fuskanci hakan ne biyo bayan rashin biyan harajin sadarwa daga bagaren Globacom. Hukumar ta kara da cewa ta ba da izinin a katse sadarwar kamfanin Globacom daga MTN Nigeria Communications Plc. A cewar Hukumar, “An sanar…
Read More
Sana’a da arziki a ma’aunin hankali suna da alaƙa ta ƙud da ƙud – Kamal

Sana’a da arziki a ma’aunin hankali suna da alaƙa ta ƙud da ƙud – Kamal

Daga AMINA YUSUF ALI Kamal Alkasim wani masani ne a fannin kasuwanci da tattalin arziki wanda ya gogu a harkar. Ga wasu shawarwari da ya bai wa masu sana'a don inganta rayuwarsu ta fannin tattalin arziki: A wannan lokacin da yawan masu sana'a kama ya yi su kara wa sana'o'insu kishiyoyi , wannan kuma ba shi da ita ya rungume ta domin ita ce silar samun arziki tilo. Duk arziki yana kunshe cikin sana'a domin ita ce hanya ingantacciya ta samunsa. Rungumar sana'o'i kanana da matsakaita ga matasanmu wannan zai zama kamar juyin juya halin yaqar talauci a wannan lokaci…
Read More