Kasuwanci

Gwamnatin Tinubu ta tsayar da ranar ganawa da su Ɗangote kan tsadar siminti

Gwamnatin Tinubu ta tsayar da ranar ganawa da su Ɗangote kan tsadar siminti

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta kira taron gaggawa tare da kamfanoni masu samar da siminti domin tattauna tashin farashin siminti a ƙasa. Kafar Nairametrics ta rawaito cewa, a halin yanzu farashin buhun siminti mai nauyin 50kg a sassan Legas ya kai N9,500. Majiyar ta ƙara da cewa a watan Janairun da ya gabata, farashin buhun simintin bai wuce N6,000 zuwa N6,500 a nan Legas ɗin ba. Tuni dai wasu ƙananan ‘yan kasuwa suka daina sayar da siminti don gudun abin da ka je ya dawo na hauhawar farashinsa. Sai dai a matsayin wani mataki…
Read More
Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya

Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Bankin Access ya ba da sanarwar naɗin Mis Bolaji Agbede a maysayin Babbar Jami'ar Zartarwar Bankin ta riƙon ƙwarya. Wannan naɗin ya biyo bayan rasuwar tsohon Babban Jami'in Zartarwar bankin mai suna Dakta Herbert Wigwe. A ranar 9 ga watan Fabrairu, 2024. Mista Wigwe ya rasu a haɗarin jirgi mai saukar ungulu tare da matarsa da ɗansa da kuma tsohuwar shugabar Kamfanin canji na Nijeriya, Abimboloa Ogunbanjo a ranar Juma'a. A wani jawabi na shugaban kwamitin daraktocin bankin ya yi ranar 12 ga Fabrairu, 2024 ya bayyana…
Read More
Tsadar Rayuwa: NLC za ta gudanar da zanga-zangar gama-gari na yini biyu

Tsadar Rayuwa: NLC za ta gudanar da zanga-zangar gama-gari na yini biyu

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta sanar da shirya zanga-zangar gama-gari na yini biyu domin nuna rashin jin daɗinta dangane da tsadar rayuwar da ake fuskanta a Nijeriya. Ƙungiyar ta ce za ta gudanar da zanga-zangar ne a ranakun 27 da 28 ga Fabrairun 2024. Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan yayin taron gaggawar da ƙungiyar ta shirya ranar Juma'a a babban ofishinta da ke Abuja. Joe ya ce, “Abin da takaici tura mu da aka yi zuwa ga ɗaukar wannan mataki, sai dai ci gaba da yin biris da ake yi game…
Read More
CBN ya dakatar da kamfanonin mai biyan kashi 100 a ƙasar waje

CBN ya dakatar da kamfanonin mai biyan kashi 100 a ƙasar waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya dakatar da kamfanonin mai na ƙasa da kasa mayar da kashi 100 na kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje zuwa ga kamfanonin ƙasashen waje a lokaci guda. Bankin ya ce, kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa na iya mayar da kashi 50 na kuɗaɗen da suka samu a matakin farko sannan sauran rabin bayan kwanaki 90. Daraktan sashen ciniki da musayar kuɗi na babban bankin, Hassan Mahmud ne ya bayyana haka a wata takardar da aka fitar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2024. Babban bankin na CBN…
Read More
Gwamnatin ƙasar Malta tana gayyatar ‘yan Nijeriya da su zo su yi mata aiki

Gwamnatin ƙasar Malta tana gayyatar ‘yan Nijeriya da su zo su yi mata aiki

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin ƙasar Malta da ke cikin nahiyar Turai ta ƙudiri niyyar ba da guraben aiki ga ƙwararrun 'yan wasu ƙasashen da ke wajen nahiyar ta Turai kamar dai 'yan Nijeriya. Inda suka sauƙaƙa hanyar neman ga masu neman aiki da ba 'yan ƙasar ta Malta ba. Wannan yunƙuri wani martani ne da ƙasar ta yi wanda ya biyo bayan kira da nuni da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi ga ƙasar a kan ta yi wani abu a game da matsalar ƙarancin ma'aikatanta. Tun a Janairun shekarar bana ne dai gwamnatin ƙasar Malta ta ƙirƙiro da wannan…
Read More
Ku yaƙi masu ɓoye abinci a ƙasa – Umarnin Tinubu ga hukumomin tsaro

Ku yaƙi masu ɓoye abinci a ƙasa – Umarnin Tinubu ga hukumomin tsaro

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bai wa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da IGP Kayode Egbetokun da Daraktan DSS, Yusuf Bichi umarni kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen yaki da masu boye abinci a kasa. Kafin wannan umarnin na Shugaba Tinubu, ‘yan Nijeriya na fama da karancin abinci ba wai don babu abincin ba, sai don wasu ‘yan kasuwa sun tara abincin sun boye wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci a sassan kasar. Sai dai a wani yunkuri da gwamnatin kasar ta yi don yaki da…
Read More
‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar abokan mu'amala da kamfanin MTN a Arewa, wato Customer Acquisition Partners CAP, sun gudanar da taron karramawa ga Hajiya Amina Usman Danbatta wacce ta riƙe Babbar Manajan Kamfanin MTN a yankin arewacin Nijeriya. Taron ya gudana ne a ranar Asabar da ta gabata a Bristol Hotel da ke cikin birnin Kano. Kafin yajiye aikinta a ranar 31 ga Oktoban 2023, Hajiya Amina ta shafe shekara 21 tana aiki da Kamfanin MTN a matsayin manaja a shiyyar Arewa. Dr. Ahmad Muhammad Sarari shi ne shugaban Kamfanin Sarari Clasiq, ya bayyana cewa dauba irin gudunmwar da…
Read More
Gwamna Lawal ya nuna alhini kan mutuwar Shugaban Access Holdings, Herbert Wigwe

Gwamna Lawal ya nuna alhini kan mutuwar Shugaban Access Holdings, Herbert Wigwe

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Babban Shugaban Kamfanin Access Holdings plc, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga masana'antar banki a Nijeriya. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ta hannun kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ranar Lahadi a Gusau, babban birnin jihar, Lawal ya nuna alhininsa game da rasuwar Herbert Wigwe. Marigayin ya ra su ne a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi da matarsa da kuma ɗansa a California ta ƙasar Amurka. A cewar Lawal, “Da rasuwar ' Wigwe, na yi rashin aboki wanda ya bada gudummawa matuƙa…
Read More
Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

Daga WAKILINMU An nuna buƙatar da ke gwamnonin jahohin ƙasar su duba tare da sauke nauyin al'umma da ya ɗauru a kansu domin samun daidaiton rayuwa Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan sha'anin tattalin arziki, Mr Tope Fasua ne ya yi wannan kira. A cewarsa, ya zama wajibi gwamnonin jihohi su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar amfani da kuɗaɗen da gwamati ke ba su wajen biyan basussukan albashi, fansho, haƙƙoƙin ‘yan kwangila da tallafi. Tope ya ci gaba da cewa, “A ƙarshen makon nan na yi bincike a kasuwanni kan hauhawar farashin ababen masarufi, abin…
Read More
Yadda farashin kayan gwari ke hauhawa a Kebbi

Yadda farashin kayan gwari ke hauhawa a Kebbi

Daga Jamil Gulma a Birnin Kebbi Kayan gwari waɗansu kayan amfanin gona ne da mafi akasarinsu a kan sarrafa su ne a miya, waɗanda kuma ke da lokacin araha da kuma tsada da suka haɗa da tumatir, ataruhu, tattasai, albasa kabeji, sure ko yakuwa (taushe) alayyafo, guro, kabushi da dai sauransu. Ana noma kayan gwari a yankunan arewacin Nijeriya, musamman a vangarorin da ke da fadama ko dausayi da qoramu, inda kusan kowacce jiha a Arewa akwai wani yanki da a ke iya samun su, sai dai kawai waɗansu yankunan sun fi waɗansu. Tsadar kayan masarufi ba sabon abu ba…
Read More