13
Aug
Mutum ne haziƙI wanda duk wanda ka tambaya shaida a kansa abu biyu yake faɗa na farko, mutum ne mai tsoron Allah sai kuma tausayi. Ya jima yana gwagwarmaya kan tallafawa al’umma da siyasa ba a iya Katsina ba a duk arewacin Nijeriya ba inda ba a ji da ganin tallafin Gwagware foundation ba. Jaridar Manhaja ta tattauna da Dr Dikko Umar Raɗɗa don jin me ne sirrin nasararsa da kuma abin da ya sa a gaba yanzu. Taƙaitaccen Tarihinka.Dr Dikko Umar Raɗɗa Gwagwaren Katsina shugaban ƙananan da matsakaitan masana’antu na ƙasa kuma shugaba na Gwagware Foundation wanda wannan gwagware…