30
May
"Babban burina na ga matsalolin mata sun ragu ko da ba su tafi gabaɗaya ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Hajiya Fatima Suleiman Baban Nana, na ɗaya daga cikin matasan ƴan siyasa mata a Jihar Gombe, wacce kuma take taka rawar gani wajen kare haƙƙoƙin mata da ba su tallafi don inganta rayuwarsu. Mace ce mai kishin ganin mata sun samu kulawa da gatan sa za su taimaki kansu da iyalinsu. A zantawar da ta yi da wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu, ta bayyana masa gwagwarmayar da take yi ƙarƙashin ƙungiyarta ta OPWIN, da abin da ya zaburar da ita…
