Labarai

Kotu ta hana Gwamna Abba rushe wasu gine-gine a Kano

Kotu ta hana Gwamna Abba rushe wasu gine-gine a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata Babbar kotu ta hana Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Kabir Yusuf ci gaba da shirin rusa gidaje da ke kan titin BUK a Ƙaramar Hukumar Gwale ta jihar. Kotun ta amince da buƙatar da aka gabatar mata a ranar 4 ga watan Yuli, wanda Ibrahim Adamu, Lauyan masu ƙara a madadin Malam Bashir Abdullahi da wasu mutum 19 suka gabatar. Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Gwamna Abba Yusuf da babban lauyan gwamnati da kuma ofishin kula da filaye da tsare-tsare da raya biranen na Jihar Kano. Tuni dai Mai Shari’a Hafsat Yahaya-Sani,…
Read More
Kwararar Hamada: Gwanatin Tarayya ta dasa itatuwa sama da miliyan 10 a jihohi 11

Kwararar Hamada: Gwanatin Tarayya ta dasa itatuwa sama da miliyan 10 a jihohi 11

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A ci gaba da ƙoƙarin da take yi na magance matsalar kwararowar hamada da ke addabar wasu jihohin ƙasar nan, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Matsalar Hamada ta Ƙasa ta dasa itatuwa sama da miliyan 10 a jihohi 11 faɗin Nijeriya. Darakta Janar na Hukumar Kula da Kwararar Hamada, (NAGGW), Dokta Yusuf Maina Bukar ne ya bayyana haka a bikin zagayowar dashen itatuwa na shekarar 2023 a Gusau, babban birnin jihar ranar Alhamis. Dokta Bukar wanda ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa na hukumar, Nasiru Ismail, ya bayyana cewa, jahohi 11 da kwararar hamada…
Read More
Cibiyata ta inganta rayuwar jama’a za ta tallafa wa ‘yan Nijeriya – Oluremi Tinubu

Cibiyata ta inganta rayuwar jama’a za ta tallafa wa ‘yan Nijeriya – Oluremi Tinubu

Daga IRAHEEM HAMZA MUHAMMAD Cibiyar Inganta Rayuwar Jama'a, wacce a Turance ake kira da suna 'Renewed Hope Initiative' (RHI) ta ƙuduri aniyar rage ƙuncin rayuwa ga al'ummar Nijeriya. Ta faɗi haka ne bayan taron hukumar gudanarwa ta cibiyar da aka gudanar a ofishinta dake cikin Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock dake Abuja. Wannan sanarwa ta biyo bayan sanarwa da kakakinta Busola Kukoyi ta fitar. Uwargidan Shugaban Ƙasa Ahmed Bola Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu wacce ita ce Shugabar cibiyar don inganta rayuwar jama'a ta ce, an kammala tsari domin ƙaddamar da shirin a jihohi 36 da babban birnin Tarayya, Abuja.…
Read More
Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

An rantsar da Eiditan Jaridar Blueprint na intanet, Amb. Ikenna Okonkwo, a matsayin Sakataren Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Nijeriya. Amb. Okonkwo ya gaji wannan matsayi ne a wajen Mr. Jude Opara bayan da ya tsaya takarar neman muƙamin ba tare da hamayya ba. Haka nan, Mr. Isaiah Benjamin na Jaridar Leadership shi ne wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙungiyar SWAN na ƙasa bayan babban taron da ƙungiyar ta gudanar a ranar Alhamis, 13 ga Yulin 2023.
Read More
‘Yan sanda sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin fashi da makami a Jihar Jigawa

‘Yan sanda sun cafke wasu mutane biyar da ake zargin fashi da makami a Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a wana samame suka gudanar a jihar. Wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Lawal Shiisu, ya fitar a ranar Laraba a Dutse, ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin waɗanda ake zargi da laifin fashin wani direban babur. Ya ce wanda abin ya ritsa da shi, Ashiru Musa, na ƙauyen Kyran, ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Fanisau. Marigayin ya bayyana cewa ‘yan bindigar biyu ɗauke da makamai…
Read More
Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a a Nijeriya

Majalisar Wakilai ta nemi a soke ƙarin kuɗin jami’a a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta umarci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), ta dakatar da ƙarin kuɗin makarantar da jami’o’i suka yi nan take. Wakilin Mazaɓar Dala dake jihar Kano, Ali Sani Madakin Gini (NNPP) ne ya gabatar da wannan ƙudirin a zauren majalisar. Madakin Gini ya ce jami’o’in gwamnatin tarayya sun nunnuka kuɗin makaranta sakamakon hauhawar farashi da ƙarancin kuɗin tafiyarwa da suke samu daga gwamnati. Ya ce daga cikin jami’o’in da suka yi wannan ƙarin akwai Jami’ar Bayero dake Kano (BUK), Jami’ar Nijeriya dake Nsukka (UNN), Jami’ar Jos, da Jami’ar Noma ta Michael…
Read More
Tinubu ne zai bayyana sabuwar ranar da za a yi ƙidayar jama’a – NPC

Tinubu ne zai bayyana sabuwar ranar da za a yi ƙidayar jama’a – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne da kansa zai bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje a Nijeriya. Shugaban hukumar, Nasir Isah Kwarra ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan ya jagoranci tawagar hukumar domin yin bayanin inda suka kwana ga Shugaba Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja. Ya ce ya zuwa yanzu, hukumar ta miƙa rahotonta ga Shugaban, kuma shi take jira ya yi nazari a kai sannan ya yanke hukunci kan lokacin da za a gudanar da ita.…
Read More
Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Mun gurfanar da Emefiele a kotu – DSS

Daga NAISR S. GWANGWAZO a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa, ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a gaban kotu. Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani kan hukuncin umarnin Babbar Kotun Abuja, wacce ta umarci hukumar da ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin mako guda ko kuma ta sake shi nan take. A yayin da Mai Shari’a Hamza Mu’azu ke yanke hukuncin kan haƙƙin bil’adama a ranar Alhamis, ya ce, cigaba da tsare mutum komai gajeren lokaci ya saɓa da haƙƙin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ‘yan sanda huɗu kwanton-ɓauna a hanyar Gusau zuwa Bunguɗu a Jihar Zamfara. ‘Yan sandan na aiki ne a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a lokacin da aka kai musu hari a daren ranar Litinin a jihar. Wani shaida a yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, an kashe huɗu daga cikin ‘yan sandan yayin harin “’Yan bindiga da ke da yawan gaske sun kashe ‘yan sanda huɗu a Bunguɗu a daren jiya; sun yi wa ‘yan sandan kwanton-ɓauna ne a hanyar Gusau Bungudu kusa da…
Read More
Gwamnan Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisba

Gwamnan Kano ya naɗa Sheikh Daurawa a matsayin Shugaban Hisba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa kan muƙamin shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano. Tuni aka miƙa wa Malam Daurawa takardar kama aiki a hukumar ofishin Sakataren Gwamnatin jihar. A watan Mayun 2019 ne Sheikh Daurawa, tare da wasu jami'an hukumar ta Hisba a wancan lokaci suka ajiye muƙamansu. Duk da dai babu cikakken bayani kan dalilin ajiye aikin nasa a wancan lokaci, an yi amannar cewa hakan ya faru ne sanadiyyar rashin jituwa da ke tsakaninsa da tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje. Sheikh Daurawa ya…
Read More