28
Nov
Daga MAHDI M. MUUHAMMAD Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da ranar fara ba da katin zaɓe na dindindin tare da ƙara gargaɗar masu karya dokokin zaɓe gabanin zaɓen 2023. Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zave na hukumar na ƙasa, Festus Okoye Esq, ya fitar da ranar Asabar a Abuja. Hukumar ta yi zamanta ne a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba, 2022, inda ta tattauna kan batutuwa da dama da suka haɗa da kwanan wata da tsarin karɓar katin zaɓe na dindindin (PVC)…