Labarai

Kotu ta tura ɗalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Kotu ta tura ɗalibin da ake tuhuma da cin zarafin Aisha Buhari gidan yari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja mai lamba 14, ta tura wani ɗalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Mohammed zuwa gidan gyaran hali na Suleja da ke Jihar Neja bisa zargin rubutun cin zarafin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari a shafinsa na Tuwita. An gurfanar da ɗalibin ne a Abuja a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba, 2022 bisa laifin zamba ta yanar gizo inda aka hana belinsa duk da cewa ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Idan ba a manta ba, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, jami’an tsaro ne…
Read More
Gwamnatin Kano ta janye dokar hana bin wasu tituna ga matuƙa baburan adaidaita sahu

Gwamnatin Kano ta janye dokar hana bin wasu tituna ga matuƙa baburan adaidaita sahu

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar taƙaita bin hanyoyin ga matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita sahu a wasu titunan Kano, Shugaban Hukumar Karota Baffa Babba Ɗan agundi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a ofisoshin sa. Ya ce “mun janye dokar ne saboda biyayyar da 'yan adaidaita suka yi ga dokar da kuma yadda al’umma suka koka akan ta."
Read More
Gwamnati za ta fara bai wa ma’aikata magidanta hutun jego

Gwamnati za ta fara bai wa ma’aikata magidanta hutun jego

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta amince ta soma bai wa ma'aikatanta magidanta hutun jego na kwana 14 a duk lokacin da matansu suka haihu. Shugabar ma'aikatan gwamnati ta ƙasa, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana haka cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin. Sanarwar ta ce bai wa ma'aikatan hutun jegon daidai yake da tanade-tanaden Kundin Dokokin Ma'aikatan Gwamnati na 2021. Gwamnati ta ce hutun na kwanakin aiki 14 ne amma ban da ranakun Asabar da Lahadi, kuma sau ɗaya a cikin shekara biyu. Yemi-Esan ta ce, sanarwar hakan ta fara aiki ne daga ranar 25 ga Nuwamban 2022.
Read More
Ganduje ya haramta a adaidaita-sahu a Kano

Ganduje ya haramta a adaidaita-sahu a Kano

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya haramta zirga-zirgar adaidaita-sahu a wasu manyan titunan Kano. Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Kano (KAROTA), wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 30 ga Nuwamba. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun hukumar KAROTA, Nabilusi Na’isa, wanda aka raba wa manema labarai ranar Talata. Titunan da aka haramta wa ’yan adaidaita-sahun bi sun haɗa da Babbar Hanyar Ahmadu Bello, hanyar Mundubawa zuwa Gazawa da kuma hanyar Tal’udu zuwa Gwarzo. Gwamnatin jihar ta maye gurbin adaidaita-sahun da motoci bas-bas guda…
Read More
Kwamishina ta buƙaci a hukunta Aisha Buhari kan badaƙalar gana wa ɗalibi azaba

Kwamishina ta buƙaci a hukunta Aisha Buhari kan badaƙalar gana wa ɗalibi azaba

Daga BASHIR ISAH Kwamishina a Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanada (PSC), Najatu Mohammed, ta yi kira da a hukunta matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, kan badaƙalar kamawa da gana wa Aminu Mohammed azaba da jami’an tsaro suka yi. Da kuma kama tsohuwar hadimar Aisha Buhari kan soshiyal midiya, Zainab Kazeem wadda ita ma aka lakaɗa mata duka kan zargin fallasa sirri. Aminu Mohammed matashi ne kuma ɗalibi a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa. Najatu ta faɗa wa jaridar Daily Nigerian cewa abin da Aisha ta yi ɗaukar doka ne a hannu, don haka ta buƙaci jami’an tsaro…
Read More
Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Ƙungiyar ɗalibai ta nemi afuwar Aisha Buhari kan kama Aminu Muhammad

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar ɗalibai ta Ƙasa (NANS) ta nemi afuwar uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha kan tsare wani ɗalibin jami’ar tarayya da ke Dutse Jigawa, Aminu Mohammed da jami’an ’yan sanda suka yi. Idan za a iya tunawa cewa, Hukumar SSS ta ce ta kama Aminu kan wani rubutu da ta wallafa a shafinsa na sada zumunta na yanar gizo da ta yi zargin ɓata sunan uwargidan shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari. A cewar rahotanni, Aminu Adamu Muhammed ya yi a watan Yunin 2022, inda ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa ‘Buhari ta ƙara nauyi sosai…
Read More
Kotu ta ɗaure Sufeto-Janar, Alkali Baba a kurkuku

Kotu ta ɗaure Sufeto-Janar, Alkali Baba a kurkuku

Daga WAKILINMU Babbar Kotun Tarayya mai zamanta Abuja, ta tura Sufeto-Janar na 'Yan Sanda, Usman Alkali Baba, zuwa kurkuku na wata uku. Kotun ta yanke wa Baba hukuncin ne saboda rashin bin umarninta. Da yake yanke hukuncin, Alƙalin Kotun, Mai Shari'a M. O. Olajuwon, ya ba da umarnin a ajiye Sufeto-Janar ɗin na tsawon wata uku har sai ya yi ɗa'a ga umarnin da da kotu ta ba tun ran 21 ga Oktoban 2011. Alƙalin ya ce idan bayan ƙarewar wata uku Baba bai aikata abin da ya kamata ba, za a sake tsare shi zuwa wani lokaci har sai…
Read More
Matashi ya nemi kotu ta hana iyayen budurwarsa aurar da ita

Matashi ya nemi kotu ta hana iyayen budurwarsa aurar da ita

Wani matashi ya yi ƙarar iyayen budurwarsa a gaban Babbar Kotun Shar’iar Musulunci da ke Hotoro a Kano yana neman kotun ta hana su aurar da ita ga wani matashi daban. Tunda farko matashin mai suna Imam Mukhtar Dala ya yi ƙarar budurwarsa Muhasin Auwal Dala da mahaifinta A.A. Dala da kakanta Sani Mai Alawayyo da kuma aminin babanta, Alhaji Audu, inda ya nemi kotu ta dakatar da auren da ake ƙoƙarin yi wa Muhasin ɗin saboda shi ne ya yi hidimar da zai aure ta. Haka kuma ya nemi a hana Muhasin Dala zuwa wurin kowane mutum don ɗaura…
Read More
Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar masu zuwa Amurka da Birtaniya su yi hattara da ɓarayi

Nijeriya ta gargaɗi ’yan ƙasar masu zuwa Amurka da Birtaniya su yi hattara da ɓarayi

Daga WAKILINMU Gwamnatin Nijeriya ta shawarci ’yan ƙasar da su zama masu kula da kayansu sosai duk lokacin da suka tashi tafiya zuwa ƙasashen Amurka da Birtaniya da sauransu, gudun faɗawa tarkon barayi. Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammad ne ya yi wannan gargaydi ran Litinin a Abuja. Ministan ya ce abin damuwa ne ganin yadda ’yan Nijeriya masu zuwa Amurka da Birtaniya da sauransu, ke faɗawa tarkon ɓarayi inda suke sace musu kudi fasfo. Ya ce, “Waɗanda abin ya shafa a baya-bayan nan su ne waɗanda suka tafi Birtaniya wanda akasarinsu aka sace musu kayayyakinsu a manyan shaguna,…
Read More
Ɗan banga ya harbe mahaifinsa yayin gwada maganin bindiga

Ɗan banga ya harbe mahaifinsa yayin gwada maganin bindiga

Wani ɗan banga ya baƙunci lahira a yayin da yake gwada maganin bindiga a Jihar Adamawa. Magidancin da ya sha maganin bindiga ya ɗora bindigarsa ce a cikinsa sannan ya tursasa wa ɗansa mai shekara 19 ya harba ta. Harba bindigar da ɗan ya yi ke da wuya ta tashi da mahaifin, ta kuma yi sanadiyyar mutuwarsa. Kakakin ’yan sanda na Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Jada ta jihar. Jami’in ya ce, su na gudanar da bincike kuma duk wanda ke da hannu a…
Read More