03
Mar
Daga AISHA ASAS Jami'an Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Neja, sun kama wasu mutum biyu ɗauke da bindigogi 27 yayin da suke bakin aiki na bincike abubuwan hawa a yankin Kontagora. Waɗanda ake zargin, Danjuma Auta ɗan shekara 35, da Daniel Danrangi mai shekara 25, dukkansu 'yan asalin Dirin Daji ne a yankin Ƙaramar Hukumar Sakaba, jihar Kebbi, sun faɗa a hannun jami'an ne a hanyar Kontagora zuwa Zuru a Litinin da ta gabata da daddare. A cewar Kwamandan Hukumar na jihar Neja, Mr. Aloye Isaac Oludare, an kama su biyun ɗauke da bindigogi AK 47…