Mata A Yau

Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta – Farida Musa Kallah

Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta – Farida Musa Kallah

"Yana da matuƙar muhimmanci iyaye su cusa wa 'ya'yansu son sana'a" (Ci gaba daga makon jiya ) Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na jaridar al'umma, Manhaja. Idan ba ku manta ba, mun yi alƙawarin kawo maku ci gaban tattaunawar da muke yi da fitacciyar 'yar kasuwa, kuma 'yar boko, Farida Musa Kallah. Tun daga farko mun fara ne da tarihin rayuwarta, kafin mu gangara kan matakan da ta hau har ya kaita ga nasara a harkar kasuwanci. Hajiya Farida Musa Kallah ta yi muhimman batutuwa kan sha’anin neman na kai, wato sana'a ta…
Read More
Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Daga AISHA ASAS (Ci gaba daga makon jiya) TAMBAYA: Ba ni shawara Asas don Allah. Maigidana na yawan cewa, Ina kama da mamatai. Ba fa fuskata da fuskarta ba, har ga jiki. Yana cewa wai idan na juya Ina tafiya sai in yi kama da ita. Idan yana son ɓata min ma sai ya ce ko fita muka yi sai an ɗauka ni mamatai ce ba mata ba. Idan aka jima bai ba ni haƙƙina ba, sai na yi magana, zai iya cewa, wai wani lokaci yana kunyar kusanta ta saboda kama da surrar jikina ke yi da ta mamatai.…
Read More
Sana’a ga mace na wanzar da zaman lafiya a aurenta – Farida Musa Kalla

Sana’a ga mace na wanzar da zaman lafiya a aurenta – Farida Musa Kalla

"Rashin sana'a ga matasa babbar illa ce ga al'umma" Daga AISHA ASAS Har zuwa yanzu ba a daina samun al'ummar da ke nuna ƙyara da tsangwama ga matan da suka yunƙura don neman na kansu a Ƙasar Hausa ba. Wasu kan la'ance su don irin sana'ar da suka zaɓa, wadda suke ganin bata dace da su ba a matsayin 'ya'ya mata ba, yayin da wasu ke yin kuɗin goro kan mata masu neman na rufa wa kai asiri, wato matan da ba su da kamun kai ne kawai ke fita nema. Duk da wannan matan da suka san ciwon kansu…
Read More
Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Haushin kaza: Kishin matar uba ga ‘ya’yan miji

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanku da jimirin karatun jaridarku ta Manhaja, mai farin jini. A wannan mako za mu tattauna ne a kan yadda kishin mata yake zarcewa daga kan kishin miji zuwa kishi a kan yaran da suka haifa. Zan yi matashiya a kan wannan karin magana: "haushin kaza huce kan dami". Wato yadda idon kishiyoyi yake rufewa ruf a kan kishi har ma su dinga ramuwa da fanshe haushin kishinsu a kan 'ya'yan miji. Haka ma wasu 'yan mijin sukan ɗauki matar uba a matsayin kishiya wadda suke kishi da gasa da ita a kan duk wasu abubuwa…
Read More
Tasirin motsa jiki ga lafiya(3)

Tasirin motsa jiki ga lafiya(3)

Daga AISHA ASAS Motsa jiki na rage ƙiba: Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan Adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake yi ko ake ci wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar ɓangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma ɓangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki…
Read More
Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Ba ni shawara Asas don Allah. Maigidana na yawan cewa, Ina kama da mamatai. Ba fa fuskata da fuskarta ba, har ga jiki. Yana cewa wai idan na juya Ina tafiya sai in yi kama da ita. Idan yana son vata min ma sai ya ce ko fita muka yi sai an ɗauka ni mamatai ce ba mata ba. Idan aka jima bai ba ni haƙƙina ba, sai na yi magana, zai iya cewa, wai wani lokaci yana kunyar kusanta ta saboda kama da surrar jikina ke yi da ta mamatai. Abin ya ishe ni wallahi.…
Read More
Na yi kuka da aka ce Sanata Binani ta faɗi zaɓe – Aisha Gombe

Na yi kuka da aka ce Sanata Binani ta faɗi zaɓe – Aisha Gombe

"Mata 'yan siyasa na shan tsangwama a tsakanin al'umma" "Soyayyar Buhari ce ta sa na shiga siyasa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata a kowanne mataki suna ba da gagarumar gudunmawa wajen harkokin raya ƙasa da cigaban dimukraxiyya. Ana iya ganin mata a ko'ina yayin da aka ce an buga gangar siyasa, inda za a yi ta faɗi tashi tare da su da sauran ýan ƙasa wajen neman goyon baya ga ýan takarar su da jam'iyyunsu na siyasa. Hajiya Aisha Usman Ahmad na daga cikin waɗannan jajirtattun mata da suke taka rawar gani a siyasar Jihar Gombe da ma Nijeriya bakiɗaya.…
Read More
Tasirin motsa jiki ga lafiya (2)

Tasirin motsa jiki ga lafiya (2)

Daga AISHA ASAS Motsa jiki na ƙara yawan jinin da ke isa ƙwaƙwalwa: Yayin da ka ke motsa jiki, ɗan aike da ke kai saƙon jiki zuwa ƙwaƙwalwa zai ƙara girma, don haka zai kai jikin wadatacce. Haka zalika, zai iya tasiri wurin halittar wasu ƙwayoyin halitta da ke da matuƙar muhimmanci a lafiyar ƙwaƙwalwa. Motsa jiki na taimakon matsalar ciwon ƙafa da hannu: Duk da cewa, an fi ɗora alhakin matsalar ciwon ƙafafu ko hannaye a ƙarancin gishiri a jikin ɗan Adam, wannan ce ke sa, matsalar ta fi yawaita a lokacin zafi, kasancewar yawan zufa da ake yi.…
Read More
Ba macen da za ta yi nasara babu namiji – Ayat Adamu

Ba macen da za ta yi nasara babu namiji – Ayat Adamu

Daga AMINA YUSUF ALI Hajiya Ayat Uba Adamu ta kasance shaharayyiyar 'yar kasuwa ta intanet wacce ta jima tana gwagwarmaya kafin ta kai inda take a halin yanzu. Wakiliyar BLUEPRINT MANHAJA, Amina Yusuf Ali, ta samu zantawa da 'yar kasuwar ta yanar gizo, kuma ɗaya daga cikin iyayen da suka kafa wata sabuwar ƙungiyar mata zalla masu kasuwancin intanet (WOVA). Sun tattauna akan rayuwarta, sana'arta, ƙungiya da sauransu. A sha karatu lafiya. BLUEPRINT MANHAJA: Za mu so mu ji cikakken sunanki.  AYAT UBA ADAMU: Bismillahirrahmanirrahim. Cikakken sunana shi ne, Hajiya Ayat uba Adamu. Yi mana bayanin wacece Hajiya Ayat Uba…
Read More
Illolin da suke fuskantar mata masu cin amanar aure

Illolin da suke fuskantar mata masu cin amanar aure

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haxuwa a wani sabon makon a filinmu na zamnatakewa wanda ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A makon da ya gabata mun fara tattaunawa a kan wannan maudu’i na abin ƙyama wato zinar matan aure. A gaskiyar Magana, matan aure da dama sun afka cikin wannan ƙazantaccen ibtila’i na satar hanya. A wancan makon mun kawo muku wasu dalilai da suke sa matan aure su ci amanar aure. Sannan mun yi alƙawarin kawo…
Read More