05
Jun
Daga AISHA ASAS Motsa jiki na rage ƙiba: Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan Adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake yi ko ake ci wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar ɓangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma ɓangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki…