Mata A Yau

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na ƙiya sai ya qi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen…
Read More
Ya zame min wajibi na yi shiga ta mutunci don ‘yan baya su koya – Hajara Ɗanyaro

Ya zame min wajibi na yi shiga ta mutunci don ‘yan baya su koya – Hajara Ɗanyaro

"Ni ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin shugabar matan Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa" Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Ɗaya daga cikin mata da suka kafa tarihi a Jihar Nasarawa, jajirtacciyar mace da ta tabbatar wa duniya mata ma za su iya a ɓangaren siyasa, Hajiya Hajara Ɗanyaro Ibrahim ta samu damar amsar gayyatar da jaridar Manhaja ta yi mata, don tattaunawa da ita a wannan shafi na Mata A Yau. Mace ce mai kamar maza, da ta iya shanye ƙalubalen da ke tattare da kutsawa cikin maza don neman abinda suke riƙe da shi, don haka…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shekara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarrashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen ba mu haihu ba, mu…
Read More
Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Shin motsa jiki na taimako ga matsalar damuwa?

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Manhaja, da fatan ba ku ƙosa da wannan darasi na atisaye ba. A yau da yardar mai dukka za mu taɓo wani ɓangare da kusan zan iya cewa ya fi adabbar mutane, amma rashin sani kan sa ayi masa wata fassarar da ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa. Da yawa daga cikin wasu matsaloli da suka dangance ciwo da muke cewa matsala ce ta mutanen ɓoye, ko sammu da jifa, zuwa duk wata damuwa da ta shafi rikeɗewar tunani, takan samu ne ta sanadiyyar damuwa.…
Read More
Rabuwar aure da ƙalubalensa

Rabuwar aure da ƙalubalensa

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da haɗuwa a wannan makon! Sannunku da jimirin karatun jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu yi magana a kan yadda wasu lokuta a rayuwar aure da zaman yake yin zafi ya ƙi daɗi, har ma su yanke shawarar su rabu da juna. Ko ɗaya ya dinga riyawa a zuciyarsa ba mafita illa ya rabu da ita ko ita ta dinga tunanin idan ba ta rabu da shi ba ba ta da sauran wani 'yanci. Eh haka ne, akwai wasu lokuta na rayuwar aure da suke zuwa ku ji sam ba kwa jin daɗin…
Read More
Babu wahala ga duk wata sana’ar da ka sa kanka – Maryam Ceetar

Babu wahala ga duk wata sana’ar da ka sa kanka – Maryam Ceetar

"Tun Ina ƙarama nake da burin neman na kaina" DAGA MUKHTAR YAKUBU A daidai lokacin da a ke ganin mata an bar su a baya wajen harkar kasuwanci da sana'o'i tare da kiraye kirayen da ƙungiyoyin kare muradun mata suke yi na mata su tashi su nemi na kan su, an samu wata jaruma a cikin mata wadda ta zama kallabi tsakanin rawuna. Maryam Isah Abubakar Ceetar mace ce da take harkokin kasuwanci da sana'o'i na kanta wadda har ta kai a yanzu tana da kamfanin gine-gine da kuma qawata gidaje, baya ga harkokin kasuwanci da take yi. Ganin yadda…
Read More
Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

Dandalin shawara: Mahaifina ya ce ba zan yi aure ba har sai na mallaki gida na kaina

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. 'Yar'uwa barka da wannan lokaci. Ya iyali. Sannu da ƙoƙari. Don Allah shawara nake nema kan matsala ta. Wallahi na yi karatu har na kammala digiri na farko, na yi bautar ƙasa har yanzu na kai na samu aiki a ƙaramar hukuma, kusan shekara ɗaya da rabi kenan. To shi ne na yi ɗan tanadi da ɗan abinda nake samu na albashi zuwa 'yar buga-buga da nake yi na haɗa lefe, na tanadi kuɗi har dubu ɗari, sannan na je ga mahaifina kan sha’anin nema min aure. Anan fa…
Read More
Ilimin sana’a kafin fara ta na da matuƙar muhimmanci – Hauwa Garba Ilah

Ilimin sana’a kafin fara ta na da matuƙar muhimmanci – Hauwa Garba Ilah

"Ba sai ka rasa ba ne za ka yi sana'a" Daga AISHA ASAS Yanayin yadda mata matasa ke zage damtse wurin neman na kai don gujewa zaman kashe wando abin a yaba ne, a kuma jinjina wa ƙoƙarin su, ganin cewa, ba su bari ƙalubale da irin kallon da al'ummarsu ke yi masu ya sare masu gwiwa ba. Bincike ya nuna cewa, adadin mata da ke neman na kai a Ƙasar Hausa na gab da cimma adadin da ke zaman banza. Wannan kuwa ba ƙaramin cigaba ne a rayuwar mata, musamman ma bayan aure, kasancewar sana'a na taka muhimmiyar rawa…
Read More
Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta – Farida Musa Kallah

Uwar da ta san daɗin sana’a ce ke koyar da ‘ya’yanta – Farida Musa Kallah

"Yana da matuƙar muhimmanci iyaye su cusa wa 'ya'yansu son sana'a" (Ci gaba daga makon jiya ) Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Gimbiya na jaridar al'umma, Manhaja. Idan ba ku manta ba, mun yi alƙawarin kawo maku ci gaban tattaunawar da muke yi da fitacciyar 'yar kasuwa, kuma 'yar boko, Farida Musa Kallah. Tun daga farko mun fara ne da tarihin rayuwarta, kafin mu gangara kan matakan da ta hau har ya kaita ga nasara a harkar kasuwanci. Hajiya Farida Musa Kallah ta yi muhimman batutuwa kan sha’anin neman na kai, wato sana'a ta…
Read More
Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Daga AISHA ASAS (Ci gaba daga makon jiya) TAMBAYA: Ba ni shawara Asas don Allah. Maigidana na yawan cewa, Ina kama da mamatai. Ba fa fuskata da fuskarta ba, har ga jiki. Yana cewa wai idan na juya Ina tafiya sai in yi kama da ita. Idan yana son ɓata min ma sai ya ce ko fita muka yi sai an ɗauka ni mamatai ce ba mata ba. Idan aka jima bai ba ni haƙƙina ba, sai na yi magana, zai iya cewa, wai wani lokaci yana kunyar kusanta ta saboda kama da surrar jikina ke yi da ta mamatai.…
Read More