21
Aug
Tare Da AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai ɗakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta vangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba…