09
Jan
Daga WAKILIN MU Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira ga 'yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la'akari da jam'iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zaɓe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zaɓe a ƙasar nan. Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwar ƙwararru na yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma'a. Kwamitin Haɗin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al'amuran Zaɓe ne ya shirya taron tare da tallafin…