Month: March 2021

NDLEA ta kama bindigogi 27 a Neja

NDLEA ta kama bindigogi 27 a Neja

Daga AISHA ASAS Jami'an Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a jihar Neja, sun kama wasu mutum biyu ɗauke da bindigogi 27 yayin da suke bakin aiki na bincike abubuwan hawa a yankin Kontagora. Waɗanda ake zargin, Danjuma Auta ɗan shekara 35, da Daniel Danrangi mai shekara 25, dukkansu 'yan asalin Dirin Daji ne a yankin Ƙaramar Hukumar Sakaba, jihar Kebbi, sun faɗa a hannun jami'an ne a hanyar Kontagora zuwa Zuru a Litinin da ta gabata da daddare. A cewar Kwamandan Hukumar na jihar Neja, Mr. Aloye Isaac Oludare, an kama su biyun ɗauke da bindigogi AK 47…
Read More
Buhari ya hana jiragen sama shawagi a Zamfara

Buhari ya hana jiragen sama shawagi a Zamfara

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dokar hana jiragen sama shawagi a Zamfara tare da haramta duka ayyukan haƙar ma'dinai a jihar. Mai bai wa Buhari shawara kan harkokin tsaro, Major General Babagana Monguno (mai murabus) ne ya bayyana haka a ranar Talata a Abuja. Inda ya ce an ɗauki matakin haka ne domin kawar da matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar. Monguno ya bayyana wa manema labarai haka ne jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa wanda ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Buhari. Wannan mataki na haramta wa jiragen…
Read More
INEC ta buƙaci Majalisar Tarayya ta maida guraben zaɓe zuwa rumfunan zaɓe

INEC ta buƙaci Majalisar Tarayya ta maida guraben zaɓe zuwa rumfunan zaɓe

 Daga WAKILINMUHukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga Majalisar Tarayya da ta amince mata ta mayar da ƙananan guraben kaɗa ƙuri'a da ke faɗin ƙasar nan zuwa cikakkun rumfunan zaɓe. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan roƙon a lokacin da ya gabatar da bayani kan yadda za a sama wa masu zaɓe rumfunan kaɗa zaɓe (wato Pulling Units, PUs) a Nijeriya, a gaban Cikakken Kwamitin Majalisar Tarayya kan Hukumar Zaɓe da Al'amuran Zaɓe, a ranar Talata a Abuja. Ya ce wasu daga cikin guraben kaɗa ƙuri'ar idan aka maida su rumfunan zaɓe, za a kuma ɗauke su…
Read More
Sarkin Kagara ya rasu

Sarkin Kagara ya rasu

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko, rasuwa. Tuni dai Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya yi jajantawa ga Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, iyalai da ma ɗaukacin al'ummar Masarautar Kagara dangane da rasuwar. Bello, ya yi addu'ar Allah Ya jiƙan marigayin da rahma, Ya sanya Aljanna makomarsa, kana ya bai wa iyalansa haƙuri da juriyar rashin. Marigayin ya rasu ne a wannan Talatar, a garin Kagara, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Rafi. An haife shi ne a ran 5 ga Afrilun 1930 a Tegina. Ya rasu ya bar 'ya'ya, mata da…
Read More
Gwamna Ikpeazu ya maida martani ga Sanata Adeyemi

Gwamna Ikpeazu ya maida martani ga Sanata Adeyemi

Daga WAKILINMU Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, ya kwatanta Sanata Samrt Adeyemi na jam'iyyar APC daga jihar Kogi da mahaukaci saboda kiran sa da ya yi da mashayi. Santa Adeyemi ya kira Gwamna Ikpeazu da mashayi ne a lokacin da ya miƙe yana tofa albarkacin baki a majalisa kan batun matsalar tsaro, inda ya ce gwaman mashayi ne wanda ke cikin ɗaya daga waɗanda ba su damu da tsaron jama'arsu ba. Da yake maida martani kan batun a wajen wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja, Ikpeazu ya ce shi dai ba ya shaye-shaye balle kuma ya zama mashayi.…
Read More
Nijeriya ta karɓi rigakafin korona na farko, Buhari da mataimakinsa za su tsayar da ranar da za a yi musu rigakafin

Nijeriya ta karɓi rigakafin korona na farko, Buhari da mataimakinsa za su tsayar da ranar da za a yi musu rigakafin

Daga AISHA ASAS A balin da ake ciki, maganin rigakafin xutar korona na AstraZeneca ya iso Nijeriya. Wannan shi ne rigakafin korona na farko da Nijeriya ta samu wanda ake sa ran za a yi wa 'yan ƙasa bayan gwamnati ta kammala tsare-tsarenta gane da rigakafin. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, za su tsayar da ranar da kowannesu zai yi allurar rigakafin cutar korona a idon duniya ta hanyar amfani da rigakafin Oxford/AstraZeneca na rukunin farko guda milyan 4 da Nijeriya ta karɓa a wannan Talata. Darakta a Hukumar Bunƙasa Kula da Lafiya na Matakin Farko na…
Read More
Yadda aka kuɓutar da ɗaliban Jangeɓe da aka yi garkuwa da su

Yadda aka kuɓutar da ɗaliban Jangeɓe da aka yi garkuwa da su

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa tubabbun 'yan fashi ne suka taimaka wa hukumomin tsaro wajen ceto ɗalibai mata na makarantar Jangeɓe da 'yan bindiga suka kwashe kwanan nan. Bayan kuɓutar da su ba tare da biyan wata diyya ba, Matawalle ya karɓi ɗaliban su 279 da asubahin Talata a birnin Gusau. A cewar Matawalle, "Wannan shi ne sakamakon shirinmu na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya tare da kunyata waɗanda ke ra'ayin cewa babu tsaro a ƙasa. "Tun Juma'a muke tattaunawa da 'yan fashin inda muka cim ma yarjejeniya ranar Litinin da yamma har aka…
Read More
Gasar ƙwallon ƙafa: Ekiti ta shirya karɓar baƙi

Gasar ƙwallon ƙafa: Ekiti ta shirya karɓar baƙi

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki jihar Ekiti ta ce ta shirya tsab domin karɓar baƙuncin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa su 16 daga jihar Kwara da na sauran jihohi daga shiyyar Kudu maso-yamma sakamakon gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da aka shirya gudanarwa a jihar. A zantawarsu da manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa na Jihar, Ekiti Bayo Olanlege, ya bayyana farin cikinsa tare da bada tabbacin cewa jihar ta shirya karɓar baƙi albarkacin gasar. Olanlege ya yi amfani da wannan dama wajen yi wa baƙinsu albishir da cewa lallai za su ji daɗin gwargwadon zaman da za su…
Read More