05
Mar
Daga FARFESA UMAR LABDO ShimfiɗaIna yin wannan rubutu a matsayina na Babban Sakataren ƙungiyar FULDAN na ƙasa. FULDAN (Fulani Development Association of Nigeria) ƙungiya ce mai fafutuka don ci gaban Fulani a fagagen ilmi, al'adu, tattalin arziki da zamantakewa. An kafa ta a shekarar 1999, tana da wakilci a yawancin jihohin ƙasar nan kuma tana da alaƙa da ƙungiyoyi takwarorinta a ƙasashe makota. Ƙungiyar tana shirya tarukan wayar da kan Fulani da koya musu sana'o'i da sabbin dabarun kiwo don inganta sana'arsu. Haka nan tana gudanar da azuzuwan yaƙi da jahilci da koyon addini a rugage da ƙauyukan Fulani. GabatarwaAl'ummar…