29
Apr
Daga FATUHU MUSTAPHA Har sau biyu 'yan bindiga na kai wa Sanata Clifford Ordia (PDP Edo ta Tsakiya) hari a Litinin da ta gabata a hanyar Okenne zuwa Lokoja da kuma hanyar Lokoja zuwa Abaji. Sanata Ordia wanda shi ne shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan Basussukan Cikin Gida da Waje, ya yi wa manema labarai bayanin yadda ya kuɓuta daga harin 'yan bindigar da suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta a kan hanyarsa ta komawa Abuja daga jihar Edo. Ya ce sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaron da ke ba shi kariya da ɓarayin, wasu 'yan sanda…