07
May
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba mamaki a iya sace kowa musamman in dai mutum na yawo a sassan arewacin Nijeriya da dare ne ko ma da rana tsaka. Wannan lamari na satar mutane don neman kuɗin fansa ta zama babbar masana'antar samun kuɗaɗe ga miyagun irin daji dama watakila wasu a cikin gari. Wata dabara ma da matafiya tsakanin Abuja da Kaduna ke yi ita ce bin jirgin ƙasa don kauce wa gamuwa da ɓarayin a titi a yankin nan na Rijana. Wannan dabarar ma akwai lokacin da ba ta ɓullewa don akwai labarin an sace mutane bayan sun sauka…