05
May
Daga AISHA ASAS 'Yan bindiga sun sako ɗaya daga cikin ɗaliban jami'ar Greenfield da suka yi garkuwa da su kwanan nan a Kaduna. Kodayake dai babu wani bayani a hukumance da ya tabbatar da hakan, amma mahaifiyar ɗalibin da ya kuɓutan, Lauritta Attahiru ta tabbatar wa manema labarai kan cewa ɗanta ya dawo gida. Sai dai Lauritta ba ta yi cikakken bayani ba dangane da yadda aka yi ɗan nata ya dawo gida ba, sai da aka biya fansa ko kuwa a'a. Wata majiya ta faɗa cewa a ranar Asabar da ta gabata aka sako ɗalibin bayan kuma mahaifiyarsa ta…