Editor

9513 Posts
Allah Ya yi wa ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello rasuwa

Allah Ya yi wa ɗan uwan Gwamna Tambuwal, Muhammadu Bello rasuwa

A yammacin jiya Talata Allah Ya yi Muhammadu Bello (Wazirin Tambuwal) rasuwa. Sanarwar rasuwar ta fito ne ta hannun ƙanin marigayin kuma gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, CFR, (Mutawallen Sakkwato). Sanarwar ta nuna Marigayin ya shafe shekaru 37 riƙe da muƙamin Wazirin Tambuwal tun bayan da ya gaji mahaifinsu, Alhaji Umar Waziri Usmanu. Kazalika, sanarwar ta ce da safiyar Larabar nan za a yi janai'zar marigayin. Gwamna Tambuwal A ƙarshe, Mutawallen Sakkwato ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, kana Ya sanya Aljannar Firdausi ita ce makomarsa.
Read More
Ban taɓa rubutu don kuɗi ba – Jidda Washa

Ban taɓa rubutu don kuɗi ba – Jidda Washa

“Kare martabar mata da yaƙi da fyaɗe ya sa na fara rubutu” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ɗaya daga cikin matasan marubuta da tauraruwar su ke haske cikin jerin marubuta mata da ke sakin rubuce rubucen su a kafafen sada zumunta na 'online', Malama Jidda Washa, wacce ta rubuta littattafai da gajerun labarai da dama da ke ɗauke da darussa daban daban na kyautata rayuwa. A tattaunawar ta da Manhaja, marubuciyar ta bayyana abin da ya fara zaburar da ita ta fara rubutu, da burin ta a harkar adabi. MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kan ki?JIDDA: Sunana Hauwa'u Adam Suleiman…
Read More
Buni ya bayyana sabuwar ranar taron APC

Buni ya bayyana sabuwar ranar taron APC

Shugaban riƙo na ƙasa na jam'iyyar APC kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sanar da sabuwar ranar da jami'yyarsu za ta gudanar da babban taronta. Idan dai za a iya tunawa, a 'yan kwanakin da suka gabata ne Buni ya gana da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda a yau ya bayyana 26 ga Fabrairun 2022 a matsayin ranar da aka tsayar don gudanar da babban taron APC. Jaridar Elanza ta ce sanarwar tsayar da sabuwra ranar taron ta fito ne Darakta-Janar na yaɗa labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed.
Read More
Shaidar kammala sakandare ta yi kaɗan ga batun tsayawa takara – Gbajabiamila

Shaidar kammala sakandare ta yi kaɗan ga batun tsayawa takara – Gbajabiamila

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa duba da zamani yau, mallakar shaidar kammala makarantar sakandare ko makamancin haka a matsayin mafi ƙarancin zurfin karatu bai wadatar ba ga duk wani mai sha'awar riƙe muƙamin gwamnati. Don haka ya yi kira da a yi wa Sashe na 131 (d) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima domin ɗaga mafi ƙarancin shaidar kartun da ya zama wajibi a mallaka kafin tsayawa takarar neman muƙaman gwamnati. A cewar Gbajabiamila, tanadin shaidar karatu mafi ƙarancin da kundin tsarin mulkin ke nunawa a yanzu abu ne…
Read More
Ƙungiyar matasa masu yaƙi da miyagun ƙwayoyi sun karrama Inuwa Waya

Ƙungiyar matasa masu yaƙi da miyagun ƙwayoyi sun karrama Inuwa Waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ƙungiyar matasa masu yaƙi da miyagun kwayoyi ta ƙasa haɗin gwiwa da ofishin mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Obi Omo Agege, sun karrama Malam Inuwa Waya bisa ƙoƙarin da yake wajen yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi. Da yake bayani bayan karramawar, Malam Inuwa Ibrahim Waya wanda jigo ne a jam'iyyar APC kuma yake neman tsayawa takarar Gwannan Kano a zave na gaba, ya ce, Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sa ilimi kyauta kuma dole, saboda haka sai an taimaka ma ta a wannan fannin, shi ya sa shima yake…
Read More
Matakan kawar da fitina lokacin ƙaro aure

Matakan kawar da fitina lokacin ƙaro aure

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum wa rahmatullah. Masu karatu sannunku da jimirin karatun shafinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Ina muku godiya da fatan alkhairi, kamar yadda koyaushe kuke yi min ta hanyar kiran waya ko saƙon tes. Haƙiƙa ku ne kuke ƙarfafa ta. A rubutun wannan mako dai za mu yi magana a kan matakan da ya kamata yan uwa maza su ɗauka yayin da suke da nufin ƙaro aure. Ko kuma gwari-gwari a ce ƙaro mata daga ɗaya zuwa biyu, har ma sama da haka. Maza da yawa suna kokawa a kan yadda…
Read More
Wasan ƙanin miji (1)

Wasan ƙanin miji (1)

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkan mu da sake haɗuwa a shafin iyali na jaridar al’umma. Allah ya kawo zaman lafiya a rayuwar gidan aurenmu, ya kuma albarkaci ‘ya’yanmu. A yau dai za mu taɓo wata al’ada ta malam Bahaushe, al’adar da ta samo asali da 'isnadin' sa mai tsayi ne a lardin Hausa. Ba ko wacce ba ce face wasar ƙanin miji. A yadda na ke ji a wurin tsofafi, al’ada ce da ta samu wurin zama a Ƙasar Hausa, har ta kai suke ganin aibata ta tamkar wani saɓo. Ita wannan al’ada ta wasa tsakanin matar yaya da…
Read More
Dokar Zaɓe: Kada ku ɗauki matsayar Buhari da rashin muhimmaci, gargaɗin Jega ga ‘yan Majalisun Tarayya

Dokar Zaɓe: Kada ku ɗauki matsayar Buhari da rashin muhimmaci, gargaɗin Jega ga ‘yan Majalisun Tarayya

Daga BASHIR ISAH Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Attahiru Jega, ya faɗa wa Majalisar Tarayya cewa ɗaukar matsayar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari game da batun yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima da rashin muhimmanci ba ita ce hanya mai ɓulewa ba ga ƙasar nan. Jega ya yi wannan furici ne a wajen wani taro kan Dokar Zaɓe ta 2021 wanda cibiyar Yiaga Africa tare da abokan hulɗarta suka shirya ranar Lahadi a Abuja. A cewar Jega, lamarin zai fi yi wa ƙasa armashi idan ta shiga sha'anin zaɓe na gaba da sabuwar dokar zaɓe, yana mai cew hakan zai…
Read More
2023: Umahi ya yi wa Tinubu gugar zana

2023: Umahi ya yi wa Tinubu gugar zana

Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ya kamata 'yan siyasar Nijeriya su tsayar da shekarun yin murabus daga harkokin siyasa maimakon su ci gaba da fafutukar neman tara kuɗi har na tsawon rayuwarsu. Gwamna Umahi ya yi waɗannan kalaman ne yayin wani shiri da gidan talabijin ɗin Channels ya yi da shi a ranar Litinin wanda ake ganin gugar zana ce ya yi ga dattijon ƙasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Cif Bola Tinubu, wanda ya nuna kwaɗayinsa kan mulkin ƙasa lamarin da, da daman 'yan ƙasa ke ra'ayin cewa ai ya tsufa game da…
Read More
Kuɗi sun zama zuciyar komai na rayuwa – Hajara Idris Dambatta

Kuɗi sun zama zuciyar komai na rayuwa – Hajara Idris Dambatta

"Ilimin ’ya mace na al'umma ne" Daga ABUBAKAR M. TAHIR Mai karatu wannan tattaunawa ce da Manhaja ta yi da Hajiya Hajara Idris Dambatta, shugabar haɗaɗɗiyar ƙungiyar 'yan mata da suka kammala makarantar kwana ta Malam Madori (MADOGSAJ). A cikin zantawar, ta kawo irin namijin ƙoƙarin da gidauniyar haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta yi wajen haɗa kan 'yan ƙungiyar gami da ƙoƙarin da suke na wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin 'ya'ya mata. Haka kuma ta kawo fafutukar da suka yi na ƙirƙirar asusun wata-wata, wanda suke gudanar da ayyukan ƙungiyar. A sha karatu lafiya: MANHAJA: Ko za ki gabatar da…
Read More