20
Jan
Daga NAFI'U SALISU Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai. Matsalar tsaro, wani al’amari ne da ya ɗauki dogon lokaci yana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya, musamman a yankin Arewacin ƙasar nan. Domin kuwa hatta ƙananan yara sun fahimci halin da ƙasa take ciki a kan rashin tsaro. Sai dai kuma wasu al’umma suna danganta laifin matsalar tsaro kacokan a kan Gwamnati, wanda hakan ya haifar da tsana mai tsanani, da faɗar baƙaƙen maganganu marasa daɗin ji a bakunan al’umma ga su shugabanni. Haka kuma wasu kan danganta matsalar rashin tsaron a kan al’umma da kuma Gwamnati. To masu…
