17
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta wasu raɗe-raɗi da ke yawo da ke bayyana cewa yana tattaunawa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje don yin sulhu. Yayin wata hira da Channels TV da yammacin ranar Lahadi. Kwankwaso ya ce ya ji daɗin ziyarar ta'aziyyar da Ganduje ya kai masa kwanakin baya, amma bayan wannan ziyara ta gaisuwa babu wata magana da ake yi a bayan fage dangane da yin sasantawa. Ya bayyana yadda alaƙarsa ta kasance da Gandujen a baya tun lokacin da ya yi mata mataimakin gwamnan Kano a zaɓen…
