Editor

9384 Posts
Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Daga FATUHU MUSTAPHA Fitaccen malamin Islman nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wata ganawar sirri tare da Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun, a Lahadin da ta gabata. Wata majiya ta kusa da taron, ta ce Gumi ya zaɓi ganawa da Chief Obasanjo ne kasancewarsa na mai faɗa a ji a cikin ƙasa kuma wanda al'umma ke girmamawa. Malamin ya labarta wa Obasanjo ziyarar da ya kai wa Fulani masu fashi a Arewacin ƙasa da zummar gwamnati ta yi wa yanayin kyakkyawar fahimta da kuma yin aiki da shawarwarin da…
Read More

Kada ‘yan Nijeriya su yanke tsammanin samun daidaiton Nijeriya – Osinbajo

Osinbajo Daga UMAR M. GOMBE Mataimakin Shugaban Ƙasa Professor Yemi Osinbajo, ya buƙaci 'yan Nijeriya da su zamo masu kyautata zato tare da fatan harkoki za su daidaita a ƙasa. Osinbajo ya faɗi haka ne yayin wata ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ibadar Easter a mujami'ar Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a Lahadin da ta gabata. A cikin sanarwar da hadiminsa kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Laolu Akande ya fitar, Osinbajo ya ce yana da yaƙinin rahma da albarkar Ubangiji za su lulluɓe Nijeriya. Sanarwar mai taken 'Saƙon bikin Easter na Osinbajo zuwa…
Read More
Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin sauya sheƙa daga jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC inda ake sa ran shugaban riƙo na APC, Mai Mala Buni ya gabatar da shi ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mai yiwuwa a kammala komai idan tawagar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Zamfara a ranar Talata domin jajanta wa gwamnan game da ibtila'in gobarar kasuwa da ya auku kwannan nan a jihar. Tun ba yau ba, wasu gwamnoni masu ci tare da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima, na daga cikin gaggan 'yan siyasar da…
Read More
Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a ci gaba da aikin rajistar katin masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni, 2021. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis. Mahmood ya ce, “Bayan mun duba waɗannan matsaloli da matakan da mu ka ɗauka don magance su, yanzu hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana Litinin, 28 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba…
Read More
Hajjin 2021: Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin yi wa maniyyata rigakafin korona

Hajjin 2021: Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin yi wa maniyyata rigakafin korona

Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano, ta ce ta ƙaddamar da shirin allurar rigakafin cutar korona ga maniyyatan Hajjin 2021 a jihar inda ta soma bada allurar ta kan ma'aikatanta. A wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami'arta ta hulda da jama'a, Hadiza Abbas Sunusi, hukumar ta ce ta soma gudanar da shirin ne a Larabar da ta gabata inda aka buɗe fagen yin allurar da fara yi wa Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Dambatta. A cewar Sakataren, an ƙaddamar da shirin yin allurar ne domin cika sharaɗin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta…
Read More
Filato: An tsige DPO bisa zargin kashe wasu makiyaya biyu

Filato: An tsige DPO bisa zargin kashe wasu makiyaya biyu

Daga BASHIR ISAH Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Filato, Edward Egbuka, ya tsige tare da tsare DPO mai kula da yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar, wato DSP Solomon Machu, bisa zargin kisan wasu makiyaya biyu a jihar. An zargi DPOn ne da kashe Musa Giwa ɗan shekara 24, da Ibrahim Sa'idu ɗan shekara 30, ta hanyar mafani da bindigabayan da 'yan bijilanti na yankin suka kama makiyayan a ƙauyen Dogon Daji tare da miƙa su ga DPOn cikin ƙoshin lafiya a Lahadin da ta gabata. Manhaja ta tattaro cewa a Alhamis da ta gabata 'yan sanda suka miƙa gawarwakin…
Read More
Duk littafin da na rubuta ba ƙagaggen labari ba ne ya faru da gaske – Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno

Duk littafin da na rubuta ba ƙagaggen labari ba ne ya faru da gaske – Fatima Ibrahim Garba Ɗanborno

*Zaluncin 'yan kasuwa ne ya durƙusar da marubutan mu - Fatima DAGA AISHA ASAS Fatima Garba Ɗanborno ba za a kira ta ɓoyayya ba musamman a wajen ma'abota karance-karancen littafan Hausa, domin ta yi fice wajen fitar da littattafai masu tarin faɗakarwa gami da ilimintarwa da kuma nuni cikin nishaɗi. Shi ya sa a wannan makon Jaridar Manhaja ta zagaya don zaƙulo wa masu karatu ita don jin wace ce ita? Me ya kai ta ga fara rubutu da shiga harkokin marubuta tsundum? Tare kuma da jin irin nasarori da faɗi-tashin da ta yi kafin ta zama cikakkiyar marubuciya? Duk…
Read More
An ceto baƙin haure 483 a gaɓar tekun Libya, inji IOM

An ceto baƙin haure 483 a gaɓar tekun Libya, inji IOM

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Kula da Sha'anin 'Yan Gudun Hijira ta Ƙasa da Ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM), ta ce baƙin haure 483 aka ceto daga gaɓar tekun Libya a yammacin ƙasar. Hukumar ta ce dogarawan tsaron tekun Libya sun yi aikin ceton baƙin ne a lokuta daban-daban. IOM na mai cewa duk da dai an bai wa baƙin taimakon gaggawa da sauran kulawar da ta dace, sai dai ta ce tashar ruwan Libya ba ta da tsaro. Ta ci gaba da cewa baƙin haure sama da 4,500 ne aka daƙile ko aka cece su a wannan shekara…
Read More
Duk namijin ƙwarai ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba – Khadija S. Mohammed

Duk namijin ƙwarai ba zai zauna da macen da za ta iya kisa ba – Khadija S. Mohammed

DAGA AISHA ASAS Wannan makon mun yi wa ma su karatun jaridarmu babban kamu a wannan shafin, domin mun samu damar tattaunawa da matar nan da ke bai wa ma'aurata da masu shirin yin aure shawarwari domin inganta zaman aurensu, har ta kai su kasance takalmin kaza. Da yake irin wannan cibiya ta Khadija Sa'ad Mohammed tamkar baƙon abu ne ga mutanen Arewacin Nijeriya, amma idan masu karatu suka biyo mu za su ji yadda baƙuwar tamu suke samun koke da jin matsalolin zamantakewar aure da kuma yadda suke bada shawara kuma a samu mafita da daidaito. Ga dai yadda…
Read More