Kasashen Waje

Nijar: Yadda gobara ta ci ƙananan yara 20 a makaranta

Nijar: Yadda gobara ta ci ƙananan yara 20 a makaranta

Daga BASHIR ISAH Ƙananan yara 'yan makaranta kimanin su 20 aka ruwaito sun halaka a ƙasar Nijar sakamakon gobarar da ta auku a wata makaranta. Wannan mummunan al'amari ya faru ne a Talatar da ta gabata a gefen Niamey, babban birnin ƙasar, inda iyaye da malamai haɗa da sauran al'ummar yankin suka kasance cikin alhini mara misaltuwa. Gobarar ta ci yaran ne a cikin azuzuwan da aka gina da katakai, kamar yadda shaidu suka bayyana. Daraktar makarantar, Habiba Gaya, cikin kuka da hawaye ta faɗa wa jaridar AFP cewa haka yaran suka ƙone a cikin gobarar. Ta ce wasu daga…
Read More

Zimbabwe: Ɗalibai 106 sun kamu da cutar korona cikin sa’o’i 24

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Zimbabwe sun nuna ya zuwa ranar Alhamis da ta gabata, an samu ɗalibai 106 daga wasu makarantun ƙasar guda biyu da suka harbu da cutar korona a cikin yini guda. Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai 51 sun kamu da cutar daga makarantar Sacred Heart GirlsHigh School da ke Esigodini, sannan ɗalibai 55 daga makarantar Umzingwane High School. Kawo yanzu, ƙasar mai yawan al'ummar da ya haura milyan 15, mutum 1,525 aka tabbatar cutar korona ta yi ajalinsu. Sai dai a daidai lokacin da aka sake buɗe makarantun ƙasar, tsoron cewa…
Read More

Bazoum ya naɗa sabbin ministocin sa a Nijar

Shugaba Bazoum Daga UMAR M. GOMBE Sabon Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya naɗa sabbin ministoci da za su yi aiki a gwamnatin sa, kamar yadda sanarwar da Sakataren Gwamnatin ƙasar ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata. Sanarwar ta ƙara da cewa, an naɗa sabbin ministoci 33, kuma shida daga cikin su mata ne. Hakan na nufin adadin ministocin ya ragu idan aka kwatanta da ministoci 43 da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaba Mahaman Issoufou. Naɗin ministocin ya faru ne a yayin da sabon Fira Ministan Jamhuriyar ta Nijar Ouhoumoudou Mahamadu ya sha rantsuwar kama…
Read More

Shugaba Ouattara ya ce Gbagbo da Ble za su iya dawo wa gida

Alassane Ouattara Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Ƙasar Kwaddebuwa, Alassane Ouattara ya ce tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo da kuma jagoran matasa ’yan gani-kashe-ni da ke mara masa baya wato Charles Ble na iya komawa gida a duk lokacin da suke buƙata, bayan da kotun duniya ta ICC ta wanke su daga laifukan da ake zargin su da aikatawa. Shugaba Ouattara, wanda ke jagorantar taron majalisar ministocin ƙasar a ranar Larabar da ta gabata, ya ce bayan dawowar sa a gida tsohon shugaba Laurent Gbagbo zai ci moriyar illahirin haƙƙoƙin da doka ta ce a bai wa tsohon shugaban ƙasar.…
Read More
An ceto baƙin haure 483 a gaɓar tekun Libya, inji IOM

An ceto baƙin haure 483 a gaɓar tekun Libya, inji IOM

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Kula da Sha'anin 'Yan Gudun Hijira ta Ƙasa da Ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM), ta ce baƙin haure 483 aka ceto daga gaɓar tekun Libya a yammacin ƙasar. Hukumar ta ce dogarawan tsaron tekun Libya sun yi aikin ceton baƙin ne a lokuta daban-daban. IOM na mai cewa duk da dai an bai wa baƙin taimakon gaggawa da sauran kulawar da ta dace, sai dai ta ce tashar ruwan Libya ba ta da tsaro. Ta ci gaba da cewa baƙin haure sama da 4,500 ne aka daƙile ko aka cece su a wannan shekara…
Read More
Shugaba Ramaphosa ya haramta sayar da giya lokacin Easter a ƙasarsa

Shugaba Ramaphosa ya haramta sayar da giya lokacin Easter a ƙasarsa

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ɗauki matakin haramta sayar da giya na kwanaki huɗu lokacin bikin Easter domin daƙile yaɗuwar cutar korona, inji RFI. Da yake jawabi ga al’ummar ƙasarsa, Shugaba Ramaohosa ya ce sun gano cewar mutanen da suka kwankwaɗi giya na aikata laifuffukan da ba su dace ba waɗanda ke yaɗa cutar korona. Don haka ya ce daga ranar juma’a zuwa Litinin masu zuwa, ba za a sayar wa mutane giyar su kai gida ba. Amma za a bar ta ga masu sha a gidajen abinci da mashaya. Mutane sama da miliyan ɗaya…
Read More
Baƙin haure 39 sun mutu a Tunisia

Baƙin haure 39 sun mutu a Tunisia

Daga FATUHU MUSTAPHA Aƙalla baƙin haure 39 ne suka rasa rayukansu a lokacin da kwale-kwale biyu suka nitse a kusa da Tunisia a ranar Talata yayin da suke ƙoƙarin tsallake kogin Bahar Rum zuwa tsibirin Lampedusa na Italiya, in ji jami'an tsaron Tunisia. Jami'in Tunisa Mohamed Zekri, ya ce masu tsaron bakin ruwa sun samu nasarar ceto wasu mutum 165, sannan ana ci gaba da neman ƙarin waɗanda suka tsira a gaɓar Sfax. Ya ƙara da cewa dukkan baƙin hauren da suka mutun 'yan Afirka ne. Jaridar Alarabiya ta ruwaito cewa, a 2019 kimanin baƙin haure 'yan Afirka su 90…
Read More
Ana ci gaba da ayyukan ceto a Equatorial Guinea

Ana ci gaba da ayyukan ceto a Equatorial Guinea

Daga MOHAMMED U. GOMBE Tun bayan aukuwar fashewar wasu abubuwa da aka samu a ƙasar Equatorial Guinea, hukumomin lafiyar ƙasar na ci gaba da yin kira ga jama’a da su bayar da gudunmawar jini da kuma buƙatar jama’a su shiga ayyukan sa-kai domin taimakawa wajen ceto rayuwar al’umma. Aƙalla mutum 15 ne suka rasu sannan wasu ɗaruruwa sun jikkata sakamakon fashewar kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar ya bayyana. Ibtila'in ya auku ne a Lahadin da ta gabata kusa da barikin sojoji a birnin Bata, inda aƙalla mutum 500 suka ji rauni. Bayanai daga ƙasar sun nuna fashe-fashen sun auku…
Read More